Katsina Ta Amince Da Siyan Motoci Masu Amfani Da Lantarki, Za Ta Gina Dogon Bene A Lagos

Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da siyan motoci masu amfani da lantarki da kekunan adaidaita sahu masu amfani da hasken rana a ƙarƙashin shirin bunƙasa sufuri na jihar.

Mataimakiyar Shugabar Hukumar Bunƙasa Kasuwanci ta Katsina (KASEDA), Aisha Aminu, ce ta bayyana haka bayan taron majalisar zartarwa ta jihar da Gwamna Dikko Radda ya jagoranta a Katsina ranar Alhamis.

Ta ce shirin yana da nufin sauƙaƙa farashin sufuri ga al’umma tare da samar da guraben ayyukan yi ga matasa.

A cewarta, kamfanin IRS na Kano da wani kamfani daban ne za su samar da motocin.

A yayin taron, an kuma amince da gina bene mai hawa 20 a Victoria Island, Jihar Legas, domin ƙara samun kuɗin shiga ga gwamnatin jihar.

Hadiza Maikuɗi, mai ba da shawara kan hulɗa da hukumomi da abokan bunƙasa ci gaba, ta ce aikin zai kammala cikin watanni 24.

Comments (0)
Add Comment