Kebbi Ta Amince Da Kashewa Ciyamomi Naira Miliyan 675 A Matsayin Alawus Na Kayan Gida

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris ya amince da fitar da kuɗi kimanin naira miliyan 675 domin bayar wa ga shugabannin ƙananan hukumomi 21 da aka zaɓa a jihar.

Babban Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, Alhaji Ahmed Idris ne ya bayyana hakan a jawabin da ya rabawa manema labarai a yau Alhamis a Birnin Kebbi.

Ahmed Idris ya rawaito Babban Sakataren Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi da Kula da Masarautu, Alhaji Mohammed Sani Umar na cewa, kuɗaɗen na amfanin shekarar 2022 zuwa ta 2024 ne.

Da yake nuna jin daɗinsa ga ƙoƙarin gwamnan, babban sakataren ya yaba masa ba wai kawai saboda samar da walwala ga mutane ba, har ma da aiwatar da aiyukan ci gaban al’ummar jihar da yake yi.

Da yake yin jawabi kan ci gaban da aka samu, Alhaji Aminu Ahmed, Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya, ALGON, reshen Jihar Kebbi kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kebbi ya yabawa gwamnan a madadin sauran shugabannin.

Ya bayar da tabbacin cewar, za a yi amfani da kuɗin wajen samar da kayan gida ga shugabannin ƙananan hukumomi, kansiloli da kuma sakatarorin ƙanannan hukumomin jihar.

Ya ƙara da cewar, alawus ɗin wani abu ne da suka jima suna jira, amma da zuwan wannan sabuwar gwamnatin, gwamnan ya amince da shi, abun da ya kira da iya jagoranci.

NAN

Jihar Kano
Comments (0)
Add Comment