Kira Ga Gwamna Ɗanmoɗi Kan Gyaran Matsalar APC A Birnin Kudu

Daga: Abubakar Ibrahim Ayuba (Habu Maja)

Ba abu ne ɓoyayye ba cewar akwai gagarumar matsala a jam’iyyarmu ta APC a Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu. Za a iya tabbatar da haka idan aka yi la’akari da irin ƙarfin da muke da shi lokacin da muka shiga zaɓe a zaɓuɓbukan da suka gabata, amma rashin haɗin kan shugabanninmu ya sa muka kasa kai wa ga nasara.

Tun kafin zaɓen 2023, APC tana da matuƙar ƙarfi a Birnin Kudu, muna da manya masu riƙe da muƙaman siyasa a ƙaramar hukuma, jiha da ƙasa. Muna da Sanata mai ci a wancan lokaci ɗan Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu. Muna da Ɗan Majalissar Wakilai mai ci a wancan lokacin ɗan Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu. Muna da Sakataren Gwamnatin Jiha, Ɗan Majalissar jiha da Kwamishinan Yaɗa Labarai da na Shari’a duk ƴan Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu. Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu da mataimakinsa da kuma kansiloli 10 cikin 11 duk na jam’iyyarmu ne, uwa uba kuma al’umma sun yarda da jam’iyyarmu amma duk da haka rarrabuwar kan da ke tsakanin manyanmu ta hana mu kai wa ga nasara.

Babu haɗin kai tsakanin yaran Faruku da na Nakudu. Babu haɗin kai tsakanin yaran Nakudu da na Engr. Magaji Da’u. Babu haɗin kai tsakanin yaran SSG na yanzu da na sauran gidaje kowa ya sa gabansa daban da na sauran. Kowa ya ware yana harkarsa daban tare da yaƙar ɗan jam’iyyarsa da ke wani gidan da ba nasa ba. Haka aka yi ta yi, kuma wannan ce ta sa muka faɗi zaɓe.

KARANTA WANNAN: Hadejawa, Auyakawa Da Hausawa Sun Manta Muhimmancin Kujerarsu Ta Wakilci A Abuja

Abin takaicin har yanzu shine, duk da mun faɗi a takara, kuma an kafa sabuwar gwamnati a jiha, har yanzu dai shugabanninmu ba su gane Annabi ya faku ba, sun ƙi su dawo su haɗa kansu. A yanzu haka babu haɗin kai tsakanin gidan SSG Bala Mamser da sauran gidaje irin na su Faruku, Engr. Dau da sauransu. Kuma har bayyana rashin haɗin kan yaran gidajen su ke yi ƙarara a social media da kafafen sadarwa.

Tabbas akwai tsananin buƙatar Mai Girma Gwamna Malam Umar Namadi Danmodi ka shigo sabgar APC kicin-kicin a Birnin Kudu domin ka gyarata. Idan har muka ci gaba da tafiya a haka to babu inda zamu je kuma jam’iyyar za ta ƙara wargajewa a Birnin Kudu.

Haka kuma Mai Girma Gwamna, ina kira gareka da ka bayar da takarar Shugaban Ƙaramar Hukuma nan gaba a Birnin Kudu ga haziƙin matashi, ƙwararre a kan al’amuran ci gaban al’umma kuma wanda al’umma ta yarda da shi. Yin hakan zai matuƙar temakawa wajen farfaɗo da kimar jam’iyyarmu da kuma samarwa Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu ci gaba.

Ina yi maka fatan alkhairi da addu’ar Allah Yai maka jagora Ya kuma ba ka nasara kan ƙudire-ƙudirenka na alkhairi ga al’ummar jiharmu Jigawa.

Daga ɗanka, Abubakar Ibrahim Ayuba (Habu Maja), Birnin Kudu

APCBirnin KuduHabu MajaJihar JigawaMalam Umar Namadi
Comments (0)
Add Comment