Kotu Ta Saki Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah, Bodejo

Alƙali Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya ya kori ƙarar zargin ta’addanci da ake yi wa Bello Bodejo, Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore biyo bayan buƙatar Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya na a kori ƙarar.

A baya dai kotun ta sanya lokacin yanke hukunci kan ƙarar, bayan kotun ta hana bayar da belin wanda ake zargin.

A zaman kotun na yau Laraba, lauyar Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Aderonke Imana, ta gabatar da buƙatar a kori zarge-zarge uku da ake yi wa Bodejo bisa dogaro da Sashi 108 na Dokar Hukunta Manyan Laifuffuka ta 2015 da kuma Sashi 174 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999.

Ta bayyana cewar Babban Lauyan Gwamnatin Tarayyar ya buƙaci da a kori ƙara saboda tabbatar da adalci.

Lauyoyin Bodejo ƙarƙashin Ahmed Raji, ba su musa buƙatar korar ƙarar ba, sai ma godewa Babban Lauyan Gwamnatin Tarayyar da su ka yi.

Wannan ya sa Justice Ekwo ya bayar da umarnin sakin Bodejo kamar yanda aka buƙata dogaro da sassan dokar da aka gabatar.

An dai kama Bodejo ne a watan Maris da ya gabata kan zarge-zarge uku da ofishin Babban Lauyan Gwamnati ke zarginsa da su, ciki har da zargin karya Dokar Karewa da Haramta Ayyukan Ta’addanci ta 2022.

Bello BodejoMiyetti Allah
Comments (0)
Add Comment