Kotu Ta Yanke Wa Mutane 3 Hukuncin Rataya A Jigawa

Babbar Kotun Jiha da zamanta a Kaugama, Jihar Jigawa, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga Suleiman Bello, Auwalu Muhammed da Yakubu Muhammed bisa samunsu da laifuka tara da suka hada da hada baki wajen yin fashi da makami.

Wadanda ake zargin an zarge su ne da kashe wani mai suna Audu Saje dan kauyen Manda da ke karamar hukumar Kaugama a Jihar Jigawa tare da sace babur din sa.

Sannan kuma an zarge su da garkuwa da wata da ake kira da Hadiza Abdullahi ta garin Marma da ke karamar hukumar Kirikasamma tare da neman kudin fansa naira miliyan 150.

Wakilin DailyTrust ya rawaito cewa, a lokacin da aka kamo wadanda aka zarga da laifuffukan an kwato bindigu uku kirar AK-47, da GPMG guda daya, da harsasai 309, da kudi naira miliyan 2 da dubu 70 da kuma babur din da suka kwace a wajen marigayi Audu Saje da ma wasu kayan laifin.

WANI LABARIN: Matar Da Ta Dabawa Mijinta Wuka Har Lahira Ta Ce Ba Ta Da Hankali

Alkalin da ya saurari karar, Justice M. M. Kaugama, lokacin da yake yanke wa masu laifin hukunci ya bayyana cewa, bincikar masu laifin da Babban Lauyan Gwamnatin Jigawa, Dr. Musa Adamu Aliyu ya jagoranta ta tabbatar da laifin ga mutane 3 da ake zargi (Suleiman Bello, Auwalu Muhammed and Yakubu Muhammed) cikin mutane hudun da aka gurfanar.

Kotun ta bayyana cewa, binciken masu laifin bai samu nasarar tabbatar da laifin garkuwa da mutane da sata a kan wadanda ake zargin ba.

Haka kuma kotun ta wanke daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Ya’u Mai Hatsi daga dukkan laifukan.

Hukuncin KisaJigawaKotu
Comments (0)
Add Comment