Kotun Saurararon Ƙararrakin Zaɓen Majalissun Tarayya da Majalissun Jiha a Kano, ta soke zaɓen da aka yi wa ɗan Majalissar Wakilai mai wakiltar Tarauni, Mukhtar Yarima ɗan jam’iyyar NNPP kan amfani da takardun bogi.
Mukhtar Yarima dai shine wanda ya lashe zaɓen da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabarairu, inda ya doke mai binsa Hafizu Kawu na jam’iyyar APC.
Hafizu Kawu ne ya shigar da ƙarar nuna rashin amincewa da nasarar da aka ce Mukhtar Yarima ya samu, inda ya ƙalubalanci cancantar takarar Mukhtar saboda yana da takardar shaidar kammala makarantar firamare ta bogi.
A hukuncin da Kotun Karɓar Ƙararrakin Zaɓen mai alƙalai uku ta yanke, ta ce takardar shaidar kammala firamaren da Mukhtar Yarima ya gabatar ga INEC ta bogi ce.
Kotun ta kuma ce, Makarantar Firamare ta Hausawa, wadda Mukhtar ya ce ita ya yi, sun nuna cewar takardar shaidar ba ta su ba ce, saboda babu sunan Mukhtar Yariman a cikin bayanansu.