Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Ƴan Majalissun Tarayya da ke zamanta a Asaba ta Jihar Delta, ta soke nasarar da Ɗan Majalissar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Aniocha/Oshimili, Mr. Ngozi Okolie ya samu a zaɓen ranar 25 ga watan Fabarairu.
Okolie wanda ɗan jam’iyyar Labour Party ne, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta bayyana shi a matsayin wanda yai nasara a wancan zaɓe.
Ku Karanta: Mafi Yawan Shugabannin Najeriya Suna Da Ƙarancin Sanin Mene Ne Ci Gaba – Obasanjo
To sai dai kuma tsohon Shugaban Marassa Rinjaye na Majalissar Wakilai, kuma ɗan takarar jam’iyyar PDP a wannan zaɓe, Ndidi Elumelu ya ƙalubalanci nasarar a gaban kotun, yana buƙatar a soke nasarar ta Okolie.
A ƙarar da Elumelu ya shigar mai lamba EPT/DL/HR/06/2023, ya ce, ba jam’iyyar Labour Party ba ce ta ɗau nauyin takarar Okolie, sannan kuma bai ajjiye aikinsa na gwamnati ba a lokacin takarar.
A hukuncinta, kotun mai alƙalai 3, wadda Alkali A.Z. Mussa ke jagoranta, ta soke nasarar Okolie bisa rashin cancanta inda ta ce wanda ya biyo bayansa a yawan ƙuri’u wato Elumelu ne yai nasara.
Kotun ta ce, Okolie bai samu ɗaukar nauyin jam’iyyar Labour Party ba yanda yake a doka, saboda shi ba ɗan jam’iyyar ba ne a daidai ranar 28 ga watan Mayu, 2022 lokacin da aka gudanar da zaɓen fidda gwani a jam’iyyar.
Kotun ta kuma ce, wanda ake ƙarar wato Okolie, bai ajjiye aikin gwamnatinsa ba domin ya tsaya takarar.