Kotun Amurka Ta Ɗaure Ƴan Najeriya Kan Laifin Damfarar Dala Miliyan 5

Wata Kotun Tarayya a Amurka ta yanke wa wasu ‘yan Najeriya biyu, Franklin Okwonna da Ebuka Umeti, hukuncin zaman gidan yari bisa laifin da suka aikata na damfara ta intanet da ta yaudari mutane sama da dala miliyan $5.

Wannan bayani ya fito ne cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin yanar gizo na Ma’aikatar Shari’a ta Amurka a ranar Talata nan.

An yanke wa Okwonna, mai shekaru 34, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara biyar da wata uku daga wata kotun tarayya a yankin Gabashin Virginia tare da umartarsa da ya biya kusan dala miliyan $5 a matsayin diyya.

Shi kuma abokin laifinsa, Umeti mai shekaru 35, an yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara 10 a ranar 27 ga watan Agusta kuma an umurce shi da ya biya kusan dala miliyan $5 a matsayin diyya.

Amurka
Comments (0)
Add Comment