Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Gwamnan Bauchi Ta Tabbatar Da Nasarar Bala Mohammed

Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Gwamnan Bauchi ta kori ƙarar da jam’iyyar APC da ɗan takararta na gwamna Sadique Abubakar su ka shigar su na ƙalubalantar nasarar da Bala Mohammed na jam’iyyar PDP ya samu a zaɓen gwamnan Jihar Bauchi na ranar 18 ga watan Maris.

Kotun ta tabbatar da nasarar da Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta, INEC  ta bai wa Bala Mohammed bayan gudanar da zaɓen.

Kotun mai alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Alƙali P.T Kwahar ta bayyana cewar, babu ƙwaƙƙwaran dalilin da zai sa ta soke zaɓen, inda ta ce, an gudanar da kaɗa ƙuri’a a zaɓen bisa tanade-tanaden doka.

A bayan bayyana nasarar Bala Mohammed ta cin zaɓen na watan Maris ne, jam’iyyar APC da ɗan takararta, tsohon Hafsan Sojojin Saman Najeriya, Sadique Abubakar su ka garzaya kotun su na buƙatar da a soke zaɓen saboda rashin bin ƙa’idoji a lokacin gudanar da shi.

Bala MohammedJihar Bauchi
Comments (0)
Add Comment