Ku Kare Kanku Daga Ƴanta’add, Gwamnan Katsina Ya Shawarci Ƴan Jiharsa

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya yi kira ga al’ummar jihar da su ɗauki matakan kariya don kare kansu daga hare-haren ƴanbindiga da ke addabar jihar.

Ya bayyana hakan ne a taron dandalin tattaunawa da aka gudanar mai taken: “Tattaunawa da Jama’a: Tsarin Kasafin Kudi na Jama’a na 2025” a yankin Daura.

A cikin wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, Radda ya nuna ɓacin ransa tare da kira ga malamai da su wayar da kan jama’a game da muhimmancin kare kai kamar yanda addinin Musulunci ya tanada.

Ya ce, “Abun takaici ne cewa wasu ƴanbindiga kaɗan su kai hari su zalunci gaba ɗaya al’umma,” yana mai nuni da cewa, “Ko su kansu ƴan bindigar suna jin tsoron mutuwa,” yana jaddada buƙatar fuskantar su kai tsaye.

Ya ƙara da cewa, “…daga cikin dukkan ƴanta’adda da ke aiki a Jihar Katsina, ba su da bindigu sama da 700. Abun takaici ne yanda wasu ƴan bindiga uku waɗanda suka galabaita za su bi mutane 1,000 su kashe su yayin da muka zuba ido kamar marasa wayo.”

Radda ya miƙa tambaya ga malamai a lokacin taron, “Menene Manzon Allah (SAW) ya umarci mutum ya yi idan wani ɗan fashi ya zo neman ransa ko dukiyarsa? Menene umarnin Allah a wannan lamarin?”

Ya kuma ce, “Wannan wulaƙanci ne! Yanda mutum zai tsaya kawai yana kallon yanda ake yi wa matarsa ko ƴarsa fyade? Menene amfanin rayuwarka bayan wannan? Mutuwa ta fi daraja fiye da irin wannan wulaƙancin.”

Ya ƙara yin kira ga al’umma da su zama cikin shiri don kare kansu daga hare-haren ƴanbindigar, yana mai cewa, “A duk lokacin da suka kawo hari, idan aka tara mutane masu yawa, za a iya fatattakar su domin su kansu suna tsoron mutuwa fiye da mu.”

Jihar Katsina
Comments (0)
Add Comment