Kukah Ya Roƙi Shugabannin APC Da Su Janye Ƙarin Kuɗin Man Fetur A Kan Ƴan Najeriya

Bishop Mathew Hassan Kukah na Cocin Katolika ta Sokoto ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar APC mai mulki da su rage farashin man fetur da ake sayarwa, yana mai cewa ƴan Najeriya na cikin halin yunwa.

Ya yi wannan jawabi ne a yau Juma’a a Abuja, lokacin da ake ƙaddamar da cibiyar The Progressive Institute (TPI).

In za a iya tunawa, an ƙara farashin litar man fetur zuwa N855 da N918 ko sama da haka dangane da wurin da ake sayarwa.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa na fatan alheri a taron APC, Kukah ya ce, “Mu ƴan Najeriya muna cikin yunwa. Ku nemo hanyar rage mana tsadar man fetur.”

Ya ƙara da cewa, “Har sai an gina dimokaradiyya a kan tushe mai inganci, in ba haka ba za mu cigaba da gini da tubalin toka. Ingancin dimokaradiyya a Najeriya na damu na. Dole ne mu gyara matsalar dimokaradiyya a Najeriya.”

Shugabannin APC a wajen taron da ke gudana a Otal din Abuja Continental, sun hada da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje; Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio wanda mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya wakilta; da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume.

Sauran sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma; gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa; ministoci; shugabannin jihohi na jam’iyyar APC da sauran manyan baki.

Tsadar Man Fetur
Comments (0)
Add Comment