Kusan Duk Mazauna Karkara A Najeriya Na Rayuwa Ne Cikin Talauci – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa fiye da kashi 75.5 cikin ɗari na mazauna karkara a Najeriya na rayuwa ne ƙasa da layin talauci, inda rahotonsa na watan Afrilun 2025 ya zayyana yadda hauhawar farashi da rashin tsaro ke ci gaba da jefa miliyoyin ƴan ƙasa cikin ƙunci.

Rahoton ya nuna cewa yayin da kashi 41.3 na mazauna birane ke fuskantar talauci, halin ya fi muni a yankunan karkara, musamman a Arewa inda ake da yawan marasa ilimi, rashin wutar lantarki da ruwan sha, da kuma rashin aikin yi.

“A shekarar 2018/19, kashi 30.9 na ƴan Najeriya na rayuwa ne da ƙasa da dala 2.15 a rana kafin ɓarkewar annobar COVID-19,” inji rahoton.

WANI LABARIN: Ƴan Ƙwadago Zasu Jinkirta Yunƙurinsu Na Mamaye Ofisoshin Jam’iyyar Labour

Ya kuma nuna cewa yankunan Arewa na fama da kashi 46.5 na talauci, yayin da yankunan Kudancin ke da kashi 13.5 kacal, inda ake da bambancin da ya kai 35.1.

Kashi 72.5 cikin ɗari na yara ƴan shekaru 0 zuwa 14 ne ke fama da talauci, inda mutane marasa ilimi ke da kashi 79.5, masu ilimi kashi 25.4.

Rahoton ya ƙara da cewa “ƙarancin samun ruwan sha, lalataccen tsarin tsaftar muhalli da rashin wuta na daga cikin abubuwan da ke haddasa ƙuncin rayuwa,” inda aka ƙididdige cewar kashi 30.9 cikin ɗari na ƴan ƙasa ba sa iya rayuwa da fiye da dala biyu a rana.

Duk da wasu gyare-gyaren tattalin arziƙi da gwamnati ke ƙoƙarin yi, Bankin Duniya ya ce hauhawar farashi na ci gaba da lalata ƙarfin sayayya da tsananta matsin lambar rayuwa musamman a birane.

Comments (0)
Add Comment