Kwanan Nan Gwamnati Za Ta Buɗe Boda Don Hada-Hadar Kasuwanci – Wani Ɗan Majalisa

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazaɓar Badagry, Mista Sesi Whingah, ya tabbatar wa al’ummar mazaɓarsa cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta buɗe iyakokin ƙasar nan don gudanar da ayyukan kasuwanci nan ba da jimawa ba.

Whingah ya bayar da wannan tabbaci ne yayin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da matasa na Badagry wanda ofishinsa ya shirya a ranar Asabar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya bayar da rahoton cewa taron ya samu taken: “Farfado da Kyakkyawar Makoma ga Badagry: Buɗe Damar Ƙarfafar Mutane da Samar da Cigaba.”

A cewar ɗan majalisar, gwamnati tana ƙoƙarin gano hanyoyin tara kuɗaɗen shiga na cikin gida.

“Wannan wata doka ce da muke ganin dole ne a yi, kuma za ta haifar da alheri.

“Gwamnatin yanzu za ta buɗe kan iyakokin don gudanar da ayyukan kasuwanci nan ba da jimawa ba; na san yana shafar mu da kuɗaɗen shigarmu. Na san irin wahalar da al’ummata ke fuskanta,” in ji shi.

Kan batun samar da wutar lantarki a wasu sassan al’ummar Badagry, ya tabbatar da cewa ma’aikatan Hukumar Samar da Wutar Lantarki na Karkara za su zo su duba wannan matsalar nan da wasu ƴan kwanaki.

Kan batun matsalolin shingen binciken hanya na jami’an tsaro, Whingah ya ce babu wani cigaba da zai zo Badagry saboda yawan shingayen binciken da aka kafa a kan titin Lagos zuwa Badagry.

“Na yi magana a kan wannan matsalar shingayen bincike masu yawa a zauren Majalisar Wakilai.

Kan nasarorin da ya samu a ofis, ya ce ya samar da ayyukan yi ga matasa 30 a Badagry a hukumomin tarayya.

“Har ila yau, muna kokarin kawo ayyuka 40 na dindindin ga matasanmu da suka cancanta na Badagry.

NAN

Comments (0)
Add Comment