Kwanannan Za A Koma Siyar Da Litar Fetur Naira 720 Saboda Faɗuwar Darajar Naira

Masu siyar da mai sun nuna cewar farshin man fetur zai tashi daga yanda yake a yanzu ya koma tsakanin naira 680 zuwa 720 a kwanaki masu zuwa matuƙar aka ci gaba da canja dala a kan naira 910 zuwa 950 a guraren canjin kuɗaɗe.

Su kuma dillalai da suke son shigo da man fetur Najeriya, dole ta sa sun dakata saboda ƙarancin kuɗaɗen waje da zasu yi amfani da su wajen shigo da man.

Wannan gargaɗi na ƴan kasuwar man na zuwa ne mako guda bayan darajar naira ta faɗi, inda ta kai naira 900 zuwa sama a kan kowacce dala ɗaya, wadda a ranar Juma’ar da gabata ma ta kai naira 945 a kan kowacce dala ɗaya.

KARANTA WANNAN: Tanaden-Tanaden Tinubu Na Sauƙaƙawa Ƴan Najeriya Ba Zasu Magance Komai Ba – Ƙungiyar Ƴan Kasuwa

Dillalan man sun ce, ƙofar CBN ta bayar da canjin kuɗaɗe ga masu shigowa ko fitarwa da kayayyaki, wadda take bayar da dala a kan naira 740 a duk lita ɗaya ba ta bayar da kuɗaɗe a halin yanzu, sanna ta gaza bayar da dala miliyan 25 zuwa 30 da ake buƙata ga masu shigo da fetur domin su shigo da shi.

Dillalan sun ce, wannan ya jawo dakatawa a ɓangaren dillalan da suke son shigowa da man fetur cikin Najeriya.

Sun ce, dillalin man fetur, Emadeb da ya samu damar shigo da man a ƴan kwanakin baya, a yanzu yana fuskantar matsala saboda faɗuwar darajar naira.

Dillalan sun ce, tashin farashin man fetur ɗin daga farashin da yake kai a yanzu dole ne, matuƙar ba naira ce ta ƙara daraja a kan dala ba.

Janye Tallafin MaiTsadar Man Fetur
Comments (0)
Add Comment