Kwankwaso Ya Zargi Gwamnatin Tinubu Da Nuna Wariya Ga Yankin Arewa

Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da fifita yankin Kudu wajen rabon albarkatun ƙasa tare da barin Arewa cikin talauci da koma baya.

A wajen taron tattaunawa kan gyaran kundin tsarin mulki da aka gudanar a Kano, Kwankwaso ya ce: “Kamar yadda bayanai ke nunawa, mafi yawan kasafin kuɗin ƙasa yanzu yana karkata ne zuwa gefe guda a wannan ƙasar.”

Ya ce irin wannan mummunan rabon ne ke haddasa matsalolin rashin tsaro, fatara da gazawar ci gaban Arewa, yana mai cewa, “Wannan rashin adalci ne ke jawo waɗannan matsaloli da muke fama da su a nan Arewa.”

Kwankwaso ya bayyana cewa mafi yawan hanyoyin Arewa suna cikin mawuyacin hali, inda ya ba da misalin hanyar Abuja zuwa Kano wadda ya kira da “ƙazamar hanya da aka fara shekaru da dama amma har yanzu ba a kammala ba.”

WANI LABARIN: Yadda Gwamna Namadi Ke Kiyaye Daidaito Tsakanin Masarautun Jigawa

Ya kuma ce: “Gwamnatin nan tana ɗaukar dukiya daga Arewa tana wurgawa wani yanki, sai a bar wasu yankunan a haka – wannan ba daidai ba ne kwata-kwata.”

Duk da cewa ya ce yana goyon bayan ci gaba a kowane yanki, ya nemi gwamnati ta gyara kuskurenta kuma ta tabbatar da adalci ga dukkan jihohi.

Ya ce: “Wannan ne lokacin da gwamnati za ta sauya, ta tabbatar wa mutane cewa gwamnati ba ta karkata gefe ɗaya ba.”

A yayin da ake fuskantar zaɓen 2027, ana ganin Kwankwaso a matsayin sabuwar rana ga manyan jam’iyyu da ke ƙoƙarin jawo shi domin samun rinjaye a Arewa.

Kwankwaso wanda ya lashe ƙananan hukumomi 38 cikin 44 a Kano a zaɓen 2023, ya zama ɗaya daga cikin fitattun jiga-jigan siyasa da APC ke nema ruwa a jallo domin fafatawa da Atiku da Obi a zaɓe mai zuwa.

Comments (0)
Add Comment