Libya Zata Gudanar Da Zaɓen Da Zai Iya Nuna Makomar Haɗin Kan Gabashi Da Yammacin Ƙasar

Libya na shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a gobe Asabar, wani abin gwaji ga demokaraɗiyya a ƙasar da ke cike da rarrabuwar kai da rashin tsaro, kamar yadda AFP ta rawaito.

Muhimman biranen gabas da suka haɗa da Benghazi, Sirte da Tobruk, sun ƙi shiga, abin da ya sake haska zurfin rarrabuwar gwamnatoci tsakanin ɓangaren Tripoli da masu goyon bayan Khalifa Haftar.

Shirin Majalissar Ɗinkin Duniya a Libya (UNSMIL) ya kira zaɓen da “samar da muƙamai na dole don kiyaye mulkin demokaraɗiyya,” amma ya gargaɗi cewa hare-haren baya-bayan nan kan ofisoshin zaɓe da rashin tsaro na iya ɓata tsarin.

Esraa Abdelmonem, wata uwa mai ƴaƴa uku, ta ce “Ƴan Libya na buƙatar su kaɗa ƙuri’a su kuma yi zaɓe cikin ƴanci ba tare da tsoro ko matsin lamba ba,” tana mai sha’awar ganin yadda yankunan da rikici ya shafa a watan Mayu za su kaɗa ƙuri’a.

Farfesa Khaled al-Montasser na al’amuran ƙasashen waje ya bayyana wannan a matsayin “zaɓe mai yanke hukunci,” yana cewa, sakamakon zai nuna ko ɓangarorin gabas da yamma “sun shirya su karɓi wakilai da ƙuri’a ta zaɓo maimakon danniya ko amfani da bindiga.”

Kusan masu jefa ƙuri’a 380,000, galibinsu daga yammacin ƙasar, ana sa ran za su fita, duk da cewa hukumar zaɓe ta HNEC ta dakatar da zaɓe a wasu mazaɓu saboda matsalolin gudanarwa, tasirin ƴan siyasa da kuma jinkirin rabon katin masu jefa kuri’a.

Haka kuma, an kai hari da bindigogi kan hedikwatar hukumar a Zliten ba tare da bayyana adadin raunukan da aka samu ba, inda UNSMIL ta ce wannan yunƙuri ne “na tsoratar da masu jefa kuri’a, ƴan takara da ma’aikatan zaɓe, da kuma hana su amfani da haƙƙinsu na siyasa.”

Comments (0)
Add Comment