Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya, NARD, ta janye yajin aikin sai baba ta gani da take yi a duk faɗin ƙasa, inda likitocin suka dawo aiki a yau Asabar.
Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, Innocent Orji ne ya tabbatar da hakan a jiya Juma’a da yamma.
Ya ce, sun janye yajin aikin ne da nufin dawowa aiki a yau Asabar da misalin ƙarfe 8 na safe, sannan kuma zasu duba irin nasarar da suka samu a sati biyun da suka ɗebe suna daka yajin.
Wannan dai na zuwa ne ƴan kwanaki kaɗan bayan likitocin sun dakatar da yin zanga-zanga a duk faɗin ƙasa domin takurawa gwamnati kan buƙatunsu.
Shugaban na NARD ya bayyana cewa, likitocin na da buƙatu takwas ne a wajen gwamnati waɗanda a cikinsu har da buƙatar ɗaukar sabbin likitocin da zasu cike guraben waɗanda suka bar aikin, ko kuma suka mutu.
KARANTA WANNAN: JIGAWA: Gwamna Namadi Ya Cire Shugabannin Asibitin Gumel
Ya ce, likitoci na shan wahala matuƙa saboda ƙarancinsu na shafar aiyukansu na bayar da temakon lafiya a Najeriya, inda ya jaddada cewar, kowa ya san cewar hakan gaskiya ne.
Ya ƙara da cewa, Gwamnatin Tarayya tun a watan Fabarairu da ya gabata ne ta samar da kwamiti da ya fito da tsare-tsaren yanda za a yi, amma har kawo wannan lokaci ba a bayyana tsare-tsaren ba.
Ya kuma bayyana cewa, har kawo wannan lokacin da suka janye yajin aikin, gwamnati ba ta biya buƙatun likitocin ba.
Tun a baya dai, shugabannin ƙungiyar NARD sun gana da sanatoci, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalissar Sanatocin, Godswill Akpabio kan buƙatun likitocin.
A ranar 25 ga watan Yulin da ya gabata ne likitocin suka shiga yajin aikin sai baba ta gani, suna buƙatar gwamnati ta biya musu buƙatunsu ciki har da ƙarin albashi.