Litar Man Fetur Zata Dawo Naira 500 Idan Matatar Mai Ta Port Harcourt Ta Fara Aiki A Kwanannan

A daidai lokacin da ma’aikatan matatar mai ta Port Harcourt ke rige-rige wajen ganin sun kammala aikin daidaita matatar domin fara fitar da tataccen mai, dillalan man fetur na shiryawa domin fara saro man fetur daga matatar.

A ranar Juma’ar da ta gabata, dillalan sun tabbatar da cewar matatar ta Port Harcourt da ke Jihar Rivers na dab da fara fitar da tataccen man fetur, inda su kai hasashen siyar da man a kan naira 500 kowacce lita.

Sun kuma bayar da tabbacin cewar, matatar mai ta Dangote zata kara saukar da farashin man fetur din ya koma ƙasa da naira 500 idan har ta fara fitar da tataccen man a watan Mayu mai kamawa.

Tun a ranar 15 ga watan Maris, 2024 ne, Shugaban Kamfanin NNPC LTD, Mele Kyari ya bayyana cewar, cikin makonni biyu daga wancan lokaci, matatar mai ta Port Harcourt zata fara aiki, yayin da ya ce matatar ta Kaduna zata fara aiki a watan Disamba na wannan shekara.

NNPCL
Comments (0)
Add Comment