Za a fara rubuta jarabawar neman ƙarin girma ta ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ta bana a ranar 14 ga watan Agusta, kamar yanda sanarwa da Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ta fitar.
Sanarwar mai ɗauke da kwanan watan 28 ga watan Yuli, 2023 ta samu sanya hannun shugaban ma’aikatar, Tukur Ingawa, sannan an tura ta ga Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa; Femi Gbajabiamila, Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume; Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folashade Yemi-Esan; Babban Akawunta na Ƙasa, Oluwatoyin Madein; dukkan manyan sakatarorin Gwamnatin Tarayya da sauransu.
Sanarwar ta buƙaci dukkan ma’aikatan da aka tantance domin rubuta jarabawar da su kula da ranakun da aka ware musu, sannan su halarci wajen rubuta jarabawar da daidai misalin ƙarfe 7 na safe.
A jadawalin zana jarabawar, ma’aikatan da ke matakin aiki na 14 zuwa 15 zasu rubuta jarabawarsu a ranakun 14 da 15 ga watan Agusta, yayinda waɗanda ke kan mataki na 15 zuwa 16 zasu rubuta ta su jarabawar a ranakun 16 da 17 ga watan Agusta; Sai kuma waɗanda ke kan mataki na 17 waɗanda zasu rubuta ta su jarbawar ranar 18 ga watan.