Ma’aikatan Lafiya Zasu Shiga Yajin Aikin Da NLC Ta Shirya Shiga Ranar Laraba

Ma’aikatan lafiya ƙarƙashin Haɗakar Ƙungiyoyin Ma’aikatan Lafiya, JOHESU, da Ƙungiyar Ma’aikatn Jiyya da Ungozoma ta Ƙasa sun ce zasu shiga yajin aikin da Ƙungiyar Ƙwadago, NLC ta shirya shiga a ranar Laraba, 2 ga watan Agusta mai zuwa.

Duk da umarnin kotu na hana ƙungiyar shiga yajin aiki a watan Yuni yana aiki, NLC ta ce ba zata naɗe hannayenta ta bar ƴan Najeriya suna ci gaba da ƙwalawa ba.

Labari Mai Alaƙa: Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

Da yake tattaunawa da wakilin PUNCH, Mataimakin Shugaban JOHESU, Dr. Obinna Ogbonna ya ce, ma’aikatan lafiya na jin raɗaɗin matsin tattalin arziƙin da ake ciki, kuma su ma suna buƙatar rayuwa mai inganci.

Ya ƙara da cewa, dukkan ƙungiyoyin ƙwadago na ƙarƙashin NLC wasu kuma na ƙarƙashin TUC, wannan ta sa idan dukkan su biyun suka ce a shiga yajin aiki to yana nufin ƙungiyoyin ma’aikatan lafiya, malaman makarantu, ma’aikatan kamfanoni da masana’antu duk zasu shiga.

JOHESUMa'aikatan LafiyaNLCYajin Aiki
Comments (0)
Add Comment