MAI MUHIMMANCI: Abubuwan Da Gwamnati Ta Gabatarwa Ƴan Ƙwadago Domin Su Janye Yajin Aiki

A yau Litinin ake tsammanin haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƴan ƙwadago da ta haɗa da NLC da TUC zasu sanar da matsayarsu ta ƙarshe kafin tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani da suka shirya a farawa a gobe Talata.

Wannan ya biyo bayan zaman tattaunawar da ƴan ƙwadagon suka yi da Gwamnatin Tarayya a yammacin jiya Lahadi, wanda a ƙarshensa, suka bayyana cewar zasu tuntuɓi rassansu na jihohi kan abubuwan da gwamnati ta gabatar musu domin yanke hukunci.

Abubuwan da gwamnatin ta aminta da aiwatarwa sun haɗa da ƙarin albashi na naira 35,000 ga dukkan ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƴan Ƙasa, Mohammed Idris ne ya bayyana alƙawuran gwamnatin a sanarwar da ya saki bayan wakilan Gwamnatin Tarayya a zaman da ƴan ƙwadago sun tuntuɓi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Mohammed ya ce, za a biya ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ƙarin ne na tsawon watanni shida.

KARIN LABARI: JERIN SUNAYE: Masu Degree Da Suka Samu Aikin Sa Kai Na J-Teach A Jigawa

Sauran abubuwan da gwamnatin ta aminta da aiwatarwa sun haɗa da gaggauta samar da motocin bas masu amfani da sinadarin gas na CNG domin sauƙaƙawa al’umma zirga-zirga saboda wahalar da suke sha bayan janye tallafin man fetur.

Haka kuma gwamnatin ta bayyana cewar tana cikin aikin samar da kuɗaɗe ga matsakaita da ƙananan ƴan kasuwa, sannan kuma za ta janye karɓar harajin VAT na tsawon watanni shida.

Gwamnatin Tarayyar ta sanar da cewar zata fara gudanar da shirin bayar da tallafin kuɗi na naira 75,000 ga gidaje miliyan 15 ta hanyar basu naira 25,000 duk wata a tsawon watanni uku da suka haɗa da Oktoba, Nuwamba da kuma Disamba.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila ne ya jagoranci zaman, yayin da Gwamnan Jihar Kwara, Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, Abdulrazak Abdulrahman da Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun suka kasance a wajen zaman.

Waɗanda suka halarta daga ɓangaren ƴan ƙwadago sun haɗa da, Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago, NLC, Joe Ajaero; Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Ƴan Kasuwa, TUC, Dr. Tommy Etim Okon; Sakataren Ƙungiyar NLC, Emma Ugboaja da kuma Sakataren Ƙungiyar TUC, Nuhu Toro da sauransu.

Akwai kuma ministocin Bola Ahmed Tinubu da suka haɗa da Wale Edun,, Simon Lalong, Nkeiruka Onyejeocha, Abubakar Atiku Bagudu, Betta Edu, da kuma Doris Uzoka-Anite.

Ita ma Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Dr. Folasade Yemi-Esan da Mai Bayar da Shawara kan Harkokin Tsaro na Ƙasa, Nuhu Ribadu sun samu halarta.

Gwamnatin TarayyaNLCTUC
Comments (0)
Add Comment