Majalisar Dattawa Ta Amince Da Dokar Ta-Ɓaci A Ribas, Da Tsige Gwamna Fubara

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya ayyana a Jihar Ribas, tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakinsa da mambobin majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.

A yayin zaman sirri da ƴan majalisar suka gudanar a yau Alhamis, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta wasiƙar da Shugaba Tinubu ya aiko, kafin a amince da ƙudirin.

Sanata Opeyemi Bamidele ne ya gabatar da ƙudirin bisa ga Dokar Majalisar Dattawa ta 135, yayin da Sanata Abba Moro ya mara masa baya.

Wannan matakin na Majalisar Dattawa ya zo ne bayan da Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin a yayin zaman ta na ranar Alhamis, ta hanyar kaɗa kuri’ar murya.

Idan za a iya tunawa, TTN NEWS ta ruwaito cewa an raba cin hanci ga ƴan majalisa domin su amince da ƙudirin, wanda ya janyo suka daga ƴan adawa da masana doka a Najeriya.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ɗan takarar jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, sun yi tir da matakin, suna masu bayyana shi a matsayin saɓa wa kundin tsarin mulki. 

Haka zalika, ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta soki dakatarwar da shugaban ƙasa ya yi wa gwamnan Ribas, inda ta bayyana cewa tsarin mulki bai ba shi ikon tsige gwamna ko majalisar dokoki ba, ko da kuwa an ayyana dokar ta-ɓaci. 

Shugaban NBA, Afam Osigwe, ya bayyana cewa Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulki ya tanadi sharuɗɗa da hanyoyin da ya dace a bi kafin ayyana dokar ta-ɓaci, domin kada a keta haƙƙin dimokuradiyya da ƴancin bil’adama. 

Ya ƙara da cewa, “Duk da cewa shugaban ƙasa na da ikon ayyana dokar ta-baci, tsarin mulki bai ba shi ikon tsige gwamna ko dakatar da majalisar dokokin jiha ba. Sashe na 188 ya fayyace hanyoyin tsige gwamna da mataimakinsa.”

Kungiyar NBA ta jaddada cewa ayyana dokar ta-ɓaci ba yana nufin rushewar gwamnati mai ci ba, don haka dakatar da gwamna da majalisar dokoki ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa.

Comments (0)
Add Comment