Majalisar Dattawa Ta Sanya Hukunci Kan Masu Fitar da Masara daga Najeriya

A ranar Laraba, Majalisar Dattawa ta amince da gyaran dokar da ta haramta fitar da masara da ba a sarrafa ba, inda ta tanadi hukuncin ɗaurin shekara guda ga waɗanda suka karya wannan doka.

Dokar, wadda ta samo asali daga Majalisar Wakilai, tana nufin hana fitar da masara mai yawa, musamman wadda ta kai ko ta haura ton ɗaya.

Ta kuma tanadi tara mai tsada daidai da kimar kayan da aka fitar ko ɗaurin shekara guda ko kuma haɗa hukuncin biyu ga waɗanda suka keta wannan doka. 

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti Central), yayin gabatar da dokar, ya bayyana muhimmancinta wajen magance matsalar ƙarancin abinci a Najeriya. 

“Wannan doka mai sauƙi ce kuma an bi dukkan matakan doka da suka dace wajen nazarinta. Ina roƙon abokan aikina su goyi bayanta,” in ji shi. 

Sanata Garba Maidoki (PDP, Kebbi South) ya gabatar da gyara don cire abubuwan da ake sarrafawa daga masara, kamar garin masara da man ganye, domin kare amfanin manoma da masana’antun cikin gida. 

Gyaran ya sami amincewa bayan ƙuri’ar jin ra’ayin bakunan ‘yan majalissar. 

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, wanda ya jagoranci zaman, ya ce barin abubuwan da ake sarrafawa daga masara zai taimaka wajen ƙirƙirar ayyukan yi. 

“Waɗannan abubuwan suna da matuƙar muhimmanci wajen samar da ayyukan yi. Cire su ya dace da manufofin tattalin arziƙinmu,” in ji Jibrin. 

Dokar da aka gyara za ta ci gaba zuwa kwamitin sulhu don daidaita bambance-bambance tsakanin Majalisar Dattawa da ta Wakilai kafin a miƙa ta ga shugaban ƙasa don rattaba hannu. 

Comments (0)
Add Comment