Domin ƙarfafa gwiwar matasa a harkar noma, reshen Jihar Jigawa na Majalisar Matasa ta Najeriya (YAN) ya kai ziyara ta girmamawa ga Dr. Saifullahi Umar, Mashawarci na Musamman kan Noma ga Gwamnatin Jihar Jigawa.
Ziyarar, wadda aka gudanar a ofishinsa, ta zama dama ga majalisar don sanin juna da tsara samar da haɗin kai domin ƙarfafa matasa ta hanyar gyara da inganta cibiyoyin koyon dabarun noma a faɗin jihar.
A lokacin ziyarar, majalisar ta yabawa Dr. Umar bisa jajircewarsa wajen ƙarfafa matasa da kuma rawar da yake takawa a matsayin jakadan matasa a tafiyar da mulki mai kyau.
“Muna alfahari da jajircewarka da ƙoƙarinka wajen bunƙasa noma wanda ake damawa da kowa a Jihar Jigawa,” inji Rt. Hon. Haruna Isah, Kakakin Majalisar Matasa kuma wakilin Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu.
Majalisar ta kuma bayyana ƙudurinta na ba wa Dr. Umar lambar yabo ta girmamawa a matsayin Uban Gida na reshen Jigawa na YAN, don karrama gagarumar gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa ayyukan noma ga matasa.
A jawabinsa, Mataimakin Kakakin Majalisar, Hon. Haruna Adamu Maje, wanda ke wakiltar Ƙaramar Hukumar Auyo, ya jaddada ƙudirin majalisar na sa ido kan dukkan ayyukan ƙarfafa matasa a harkar noma don tabbatar da adalci, gaskiya, da daidaito.
Ya kuma buƙaci Dr. Umar da ya ƙara himma wajen samar da ƙarin dama ga matasa, yana mai cewa, “Duk da cewa mun yaba da nasarorin da ka cimma a yanzu, muna kiranka da ka ƙara jajircewa wajen bunƙasa harkar noma da taimakawa matasa masu dogaro da ita.”
Kwamitin mai mambobi tara, wanda Rt. Hon. Haruna Isah ke jagoranta, ya ƙunshi mutane fitattu kamar Hon. Kamilu Musa Maigoro, Shugaban Masu Rinjaye kuma wakilin Gwaram; Hon. Bashir Aliyu Kwaimawa, Mataimakin Sakatare kuma wakilin Dutse; da sauran wakilai daga ƙananan hukumomi daban-daban a Jihar Jigawa.
Dr. Umar ya nuna godiyarsa ga majalisar bisa karramawar, tare da alƙawarin cigaba da aiki don bunƙasa noma mai ɗorewa da ƙarfafa matasa a Jihar Jigawa.
Ziyarar ta zama wani muhimmin mataki na ƙarfafa haɗinkai tsakanin jami’an gwamnati da wakilan matasa, da kuma kafa tubali na tafiyar da mulki mai adalci da tasiri a Jihar Jigawa.