Wani ɗan majalisar wakilai, Bayo Balogun, ya bayyana cewa za a yi gyara ga kundin tsarin mulkin Najeriya domin sanya Kotun Daukaka Ƙara a matsayin matakin ƙarshe na sauraron ƙarar zaɓen gwamna a ƙasar.
Balogun, wanda shi ne shugaban kwamitin Majalisar Wakilai kan Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na Channels TV, inda ya ce wannan sauyi zai rage yawan matakan shari’a da ake bi bayan zaɓukan gwamnoni.
A cewarsa, “Abu ɗaya da wannan doka za ta amfanar da shi, shi ne yayin da ake sauraron na majalisun dokoki a kotun sauraron ƙarar zaɓe, na shugaban ƙasa da gwamna za su kasance a Kotun Daukaka Ƙara.”
Ya ƙara da cewa, “Abin da muke ƙoƙarin yi yanzu shi ne rage lokacin da ake bai wa kotu daga kwanaki 180 zuwa 90, sannan ɗaukaka ƙara ya zama kwanaki 50 ne kawai.”
Balogun ya bayyana cewa akwai kwanaki 21 don shigar da ƙara da kuma kwanaki 14 na ɗaukaka ƙara, wanda idan aka haɗa zai kai kwanaki 185 kafin rantsar da sabon gwamna.
Ya ce, “Da zarar mun cire wannan daga kundin tsarin mulki, za mu saka shi a cikin dokar zaɓe, domin hakan zai tilasta wa INEC gudanar da zaɓe tun kafin watan Fabrairu.”
Wannan ƙudurin, wanda Nnamdi Ezechi ke ɗaukar nauyinsa, zai kawar da damar ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli a shari’o’in zaɓen gwamna.
Yanzu haka, tsarin na bai wa waɗanda ke shari’a damar kai ƙara daga kotun sauraron ƙarar zaɓe zuwa Kotun Daukaka Ƙara sannan zuwa Kotun Ƙoli, amma gyaran zai dakatar da wannan, ya sanya kotu ta biyu a mataki na ƙarshe a shari’ar gwamna kamar dai shari’ar ƴan majalissa.