Majalissar Dinkin Duniya Za Ta Duba Dakatarwar Da Aka Yi Wa Sanata Natasha

Shugabar Kungiyar Majalisun Duniya (IPU), Tulia Ackson, ta tabbatar da cewa za a bi ka’ida wajen duba korafin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yankin Kogi Central dangane da dakatar da ita daga majalisar dattawan Najeriya.

Ackson ta bayyana hakan ne yayin da Natasha ta roƙi IPU da Majalisar Ɗinkin Duniya su shiga tsakani kan abin da ta kira dakatarwar rashin adalci.

Da take magana a zaman mata ‘yan majalisa a taron IPU a ranar Talata, Sanatar ta bayyana cewa an dakatar da ita ne domin hana ta yin magana.

“Na zo ne da zuciya cike da damuwa daga Najeriya. Amma da farko, ina neman afuwa ga mambobi masu girma – ban zo nan don cin mutuncin ƙasata ba. Na zo ne don neman taimako ga matan Najeriya,” in ji ta.

Ta ce an dakatar da ita ne saboda ƙorafi da ta shigar kan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, dangane da zargin cin zarafi da neman yin lalata da ita.

“Na yi imani cewa gabatar da ƙorafi zai kawo bincike na gaskiya da adalci, amma maimakon haka, an yi min shiru kuma an dakatar da ni,” in ji ta.

A cewar ta, an hana ta tsaro, an karɓe motocinta na ofis, an dakatar da albashinta, tare da hana ta shiga harabar majalisa.

“Na tsawon watanni shida, ba a yarda in bayyana kaina a matsayin sanata, ko a gida ko a ƙasa da ƙasa ba,” in ji ta.

Ta bukaci kungiyoyin dimokuraɗiyya na duniya su shiga tsakani, tana mai cewa: “Idan za a yi wa sanata mace irin wannan cin zarafi a bainar jama’a, me zai hana a yi wa sauran mata na yau da kullum a wuraren aiki da makarantu?”

Da take mayar da martani, Ackson ta ce IPU za ta duba lamarin ta hanyar jin bayanai daga ɓangarorin biyu kafin ɗaukar mataki.

“Mun ji ƙorafinta, kuma matsayinmu a IPU shi ne mu saurari kowanne ɓangare kafin mu yanke hukunci,” in ji Ackson.

Comments (0)
Add Comment