Makaho Bai San Ana Ganin Sa Ba…!

Daga: Mukhtar Abdullahi Birnin Kudu

Daga lokacin da aka rantsar da majalisa ta goma a kasarnan, abubuwa da yawa sun faru waɗanda ya kamata ƴan majalisar su gabatar da ƙudurori na taka birki ga waɗanda ke buƙatar hakan da neman aiwatar da waɗanda ke buƙatar aiwatarwa.

Kasancewar akwai sabbin yankan rake a majalisun da kuma waɗanda su kai shura wajen ɗumama kujera, wane yunƙuri ƙungiyoyin cigaban al’umma na mazaɓun da ƴan majalisar ke rawa da bazarsu suka taka wajen dawo da hankulan su jikin su?

Batun janye tallafin mai da ake ta kwalalazon zai gallazawa talaka da batun janye tallafin karatu da tuni jami’o’i da yawa suka ninninka kuɗin ga dalibai ga kuma tsarin ba da rancen karatu mai cike da shubuha, baya ga ware wasu kuɗaɗe na tallafi, koda yake ƴan majalisar ma sun ja kasonsu, ga kuma ciyo bashin dala miliyan ɗari takwas da ware maƙudan kuɗaɗen sayen motoci ga su kansu ƴan majalisar da kuma sake karya darajar naira.

Ba lallai ne fa hankalinsu ya kai ga komai ba musamman a ƙasa irin Nigeria da kusan kowa ke da ɗabi’ar gafiya…

Yana da wahala ka ji ƙungiyoyin cigaba imma na mazaɓu, ƙananan hukumomi ko ma jiha na fafutukar zama da yan majalisar don fahimtar da su a yaren da zasu fi ganewa sarai-sarai.

Ƙungiyoyin da kawai ake jin amonsu jifa-jifa sune waɗanda ke aiki a matakin shiyya ko ƙasa baki ɗaya ko kuma waɗanda ke da alaƙa da ƙungiyoyi masu zaman kansu na duniya.

Rashin yin hakan a fahimta irin tawa dai-dai yake da batun nan na idan ɓera da sata….

Wani zai ce su ƴan majalisar ai ba mahaukata ba ne sun san abinda ya kamata su yi, a nan sai na ce eh, lallai masu hankali ne amma ba irin nawa da naka ba! Ashe kenan suna buƙatar tunatarwa ko ankararwa.

Ko wa’azi fa da malamai ke yi kaso 80% na waɗanda ke sauraro ba wai ba su sani bane, ana tunatar da su ne.

Daga: Mukhtar Abdullahi Birnin Kudu

Majalissar TarayyaMukhtar Abdullahi Birnin Kudu
Comments (0)
Add Comment