Mamakon Ruwan Sama Ya Kashe Mutane 33 Tare Da Ɓatar Da 18 A Beijing

Wani mamakon ruwan saman da ba a taɓa ganin irinsa ba a Beijing ta Ƙasar China a yau Laraba, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 33 da kuma ɓatar da wasu su 18, in ji jami’an gwamnatin ƙasar.

Jami’an sun ƙara da cewar, mamakon ruwan saman ya lalata gine-gine tare da hanyoyi a babban birnin ƙasar Chinan da maƙotansa.

Jami’an sun ce mutuwar mutane 33 ta samo asali ne daga ambaliyar ruwa da rugujewar gine-gine da mamakon ruwan saman ya jawo.

Ma’aikatar Bayar da Agajin Gaggawa ta China ta bayyana cewa, a watan da ya gabata an samu mutuwa ko ɓacewar mutane aƙalla 142, abin da ta alaƙanta da ambaliyar ruwa da kuma sauyin yanayi.

Ambaliyar RuwaBeijing
Comments (0)
Add Comment