Tsohon shugaban jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Ralph Nwosu, ya bayyana cewa aƙalla mutane bakwai da suka fito daga babbar haɗakar ƴan adawa ne ake ƙwadaitar da su tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu.
Nwosu ya bayyana hakan ne yayin da ake ci gaba da raɗe-raɗin cewa wasu ƙungiyoyin siyasa daga Arewacin Najeriya na marawa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a 2023, Peter Obi, baya don ya yi mulki na wa’adin shekara huɗu kacal.
Haɗakar ƴan adawan, wadda Atiku Abubakar da Peter Obi ke jagoranta, ta amince da jam’iyyar ADC a matsayin dandamalin siyasar da za a yi amfani da shi wajen fafatawa a zaɓen 2027.
A wata hira da Sunday PUNCH, Nwosu ya ce akwai shahararrun shugabannin haɗakar da ake da burin su zama ƴan takarar shugaban ƙasa, da suka haɗa da Atiku, Obi, Rotimi Amaechi, Nasir El-Rufai, Rauf Aregbesola, da Bamidele Ajadi.
WANI LABARIN: Ribadu Ya Ce Mutane 47,000 Ne Suka Mutu A Arewa Saboda Matsalar Tsaro
“Duk wani ɗan haɗakar na da ƴancin bayyana ra’ayinsa, akwai waɗanda ke so Aregbesola ya tsaya takara, wasu na goyon bayan Ajadi, akwai kuma na Amaechi da El-Rufai har ma da na Sule Lamido,” in ji shi.
Ya ce jam’iyyar ADC za ta buɗe tsarin zaɓen ɗan takara don bai wa kowa damar gwada farin jinin sa.
Nwosu ya bayyana cewa haɗakar siyasar da suka kafa yanzu ta fi kowace jam’iyya a Najeriya ƙarfi, inda ya ce “fiye da kashi 95 cikin 100 na PDP sun haɗu da mu tare da magoya bayansu na ƙasa, APC ta rasa kashi 35 cikin 100, LP kuwa fiye da kashi 80 cikin 100 na magoya bayansu na tare da mu.”
A cewarsa, “wannan yunƙuri ba wai kawai don samun mulki ba ne, muna so mu ceto Najeriya daga ɗakin karɓar ɗaukin gaggawa (ICU) ne zuwa sahun ƙasashen da ake kallo da daraja a duniya.”
Ya kuma ce goyon bayan da haɗakar ke samu daga matasa da tsofaffi da kuma sauran al’umma yana ƙara nuna cewa sabuwar siyasar da za su kawo ba ta dogara da sunaye ba ne, sai da shugabanci na gaskiya da kishin ƙasa.