Masu Farauta 13 Sun Ɓace, Bayan Faɗawa Maɓoyar Lakurawa A Sokoto

Aƙalla mutane 13 da ake kyautata zaton masu farauta ne, sun ɓace bayan wasu da ake zargin ƴan ta’adda ne daga ƙungiyar Lakurawa suka kai musu hari a dajin Hurumi da ke yankin Talewa, ƙaramar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto.

An tattaro cewa masu farautar sun fito ne daga yankuna daban-daban na Tangaza da Gwadabawa inda suka shiga dajin domin farauta, duk da gargaɗin hukumomi kan barazanar da ke cikin yankin.

Majiyoyi sun bayyana cewa masu farautar sun shiga har cikin maɓoyar ‘yan ta’addan ne ɗauke da bindigogin gargajiya da kuma karnukan farauta, lamarin da ya janyo rikici.

WANI LABARIN: Akwai Babbar Illa Tattare Da Barin Waya Kusa Kai Yayin Yin Bacci, In Ji Wani Masani

“An riga an gano gawarwaki uku, yayin da mutane goma suka ɓata har yanzu. Wasu sun samu nasarar dawowa gida,” in ji wani mazaunin yankin Tangaza da ya buƙaci a sakaya sunansa.

Wani jami’in gwamnati ya bayyana cewa ƴan ta’addan sun yi amfani da farautar a matsayin tarkon janyo dakarun tsaro domin kai musu hari, yana mai cewa: “Burin su bai kasance masu farautar ba; sojoji ne.”

A ranar Juma’a, ƴan ta’addan sun sake kai hari a ƙauyen Magonho, amma sojoji sun daƙile harin tare da ƙwato dabbobin da aka sace, sai dai daga bisani ƴan ta’addar suka dawo suka tarwatsa ƙarfen MTN, lamarin da ya hana sadarwa a yankin.

Ghazzali Aliyu Rakah, mai ba shugaban ƙaramar hukumar Tangaza shawara kan harkokin tsaro, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa har yanzu ana ci gaba da nemo gawarwaki da waɗanda suka ɓace, duk da ƙarancin kayan aiki da jami’an tsaro.

Comments (0)
Add Comment