Masu Juna-Biyu Na Fuskantar Karancin Abinci A Kasashe Matalauta – Majalissar Dinkin Duniya

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce adadin mata da ‘yan matan da ke da juna-biyu waɗanda ke fuskantar ƙarancin abinci mai gina jiki ya ƙaru da kashi 25 cikin 100 a ƙasashe matalauta kamar Somaliya da Habasha da kuma Afghanistan.

UNICEF ya ƙiyasta cewa fiye da mata da ‘yan mata biliyan ɗaya a sassan duniya na fama da ƙarancin abinci mai gina jiki.

WANI LABARIN: Wasu Bankunan Sun Fara Sakin Tsoffin Kudi Na Naira 1000 Da 500 Ga Kostomominsu

Asusun ya bayyana cewa matsalolin da aka shiga a duniya shekaru biyu da suka wuce ciki har da yaƙe-yaƙe da kuma annobar Korona su ne suka ƙara ta’azzara shigar mata cikin ƙangin yunwa.

UNICEF ya buƙaci ƙasashen duniya da su sanya batun samar da isasshen abinci a duniya a dukkan farkon lamuransu da kuma taimaka wa shirye-shiryen samar da abincin da suka gaza gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

BBC

AbinciJuna-BiyuUNICEF
Comments (0)
Add Comment