Matar Gwamna Ta Farko A Jihar Kano, Ladi Bako Ta Rasu

Ladi Bako, Matar gwamnan Jihar Kano na Farko, Audu Bako ta rasu tana da shekaru 93 a duniya.

‘Yarta Zainab Bako ce ta tabbatar da rasuwar mahaifiyartata ga DAILY NIGERIAN a yau Laraba, inda ta ce tsohuwa mai ran karfen ta rasu a asibitin Prime Specialist Hospital da ke Kano bayan fama da jinya.

Za a yi jana’izarta a Kofar Kudu da ke Fadar Sarkin Kano.

An nada mijin marigayiyar, Audu Bako a matsayin gwamnan Kano na farko a mulkin soja a tsakanin watan May na 1967 zuwa watan July na 1975.

Ya kawo gagarumin ci gaba a jihar tare da gina ma’aikatu da dama.

Audu BakoLadi Bako
Comments (0)
Add Comment