Matar Tinubu, Remi, Ta Laƙume Naira Miliyan 701 A Tafiye-Tafiye Cikin Wata 3

Gwamnatin Tarayya ta kashe kimanin naira miliyan 701 kan tafiye-tafiyen matar shugaban ƙasa Remi Tinubu, zuwa ƙasashen waje biyar cikin watanni uku, in ji wani rahoto da jaridar Saturday Punch ta wallafa.

A shekarar 2023, an ware naira biliyan 1.5 don sayen motocin ofishin uwargidan shugaban ƙasar, kamar yanda aka tanada a cikin ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi na naira tiriliyan 2.1 da majalisar dokoki ta amince dashi.

Sai dai kuma, tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya ce kasafin naira biliyan 1.5 na motocin ya shafi fadar shugaban ƙasa gaba ɗaya ne ba wai iya ofishin matar shugaban ƙasa ba.

Binciken da aka gudanar ta hanyar GovSpend ya nuna cewa gwamnati ta fitar da naira miliyan 700 daga asusun fadar shugaban ƙasa don tafiye-tafiyen matar shugaban ƙasa zuwa ƙasashe irin su Amurka, Faransa, Mozambique, da kuma Ethiopia.

A cikin watan Mayun shekarar nan ta 2024, gwamnati ta kashe naira miliyan 314 wajen shirya tarurrukan matar shugaban ƙasar da suka shafi matasa, mata, da yara, tare da bayar da kwangilar ƙawata wajen taro ga Rock of Ages Total Events Centre Ltd da Makeway Nigeria Limited.

Cibiyar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta CACOL ta bayyana cewa kashe irin wannan kuɗin kan ofishin da kundin tsarin mulki bai amince da shi ba, ba daidai ba ne, kuma ya nuna alamar rashin ƙwarewar ƴan majalisar dokoki.

CACOL ta yi kira ga ƴan Najeriya su ci gaba da yin kira don gyaruwar irin waɗannan lamuran, domin a daina kashe kuɗaɗen al’umma a kan abubuwan da ba su da amfani ga jama’a.

Comments (0)
Add Comment