Matasan APC a Jigawa Sun Nemi Shugaba Tinubu Ya Sauke Ministan Tsaro Badaru 

Ƙungiyar Matasa ta Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba nadin da yai wa Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, bisa rashin gamsuwa da aikinsa da kuma zargin rashin biyayya ga jam’iyyar. 

Yayin wata tattaunawa da manema labarai da magoya baya a Dutse, babban birnin jihar, a ranar Juma’a, ko’odinetan ƙungiyar, Ahmad Magaji Bashir, ya zargi ministan da yin abin da ke tauye ƙoƙarin APC a Jigawa tare da bata sunan jam’iyyar. 

“Mun yi matuƙar baƙin ciki da gazawar Badaru wajen goyon bayan manufofin jam’iyyar a Jigawa. Ayyukansa sun fi kama da na jam’iyyar adawa ta PDP, maimakon kare muradun APC,” in ji Bashir. 

Ƙungiyar ta bayyana wasu matsaloli da suka haɗa da rashin goyon bayan da ake zargin Badaru ba ya bayarwa ga ‘yan APC a Jigawa da kuma fifikon da yake bai wa masu ruwa da tsaki na PDP.

Haka kuma, ƙungiyar ta jaddada rahotannin da ke cewa an lalata allunan APC da ke nuna Shugaba Tinubu da Mataimakinsa Shettima, tana mai zargin cewa Badaru yana da hannu cikin lamarin.

“Muna cikin damuwa matuƙa kan rashin jajircewar ministan ga ƙa’idoji da manufofin APC. Ayyukansa suna da alaƙa da abin da ke cin karo da burin jam’iyyar a Jigawa da ma Najeriya baki ɗaya,” a cewar Bashir. 

Ƙungiyar ta nuna tsoron cewa ci gaba da rike Badaru a matsayin Minista a gwamnatin Tinubu na iya illata kimar APC a Jigawa da ma ƙasa baki ɗaya. 

Sun yi kira ga shugaban ƙasa da ya dauki matakin gaggawa kan lamarin. 

“Muna roƙon Shugaba Tinubu da ya sake duba nadin Badaru a matsayin Ministan Tsaro. Ci gaba da barinsa a wannan matsayin zai iya kassara haɗin kan jam’iyya da kuma cika alkawuran da aka yi wa al’umma,” ƙungiyar ta bayyana. 

Duk da haka, ƙungiyar matasan ta sake jaddada goyon bayanta ga gwamnatin Tinubu, amma ta yi kira da a samar da shugabanci mai ƙarfi da tasiri a cikin APC domin dawo da kwarin gwiwa da haɗin kai tsakanin mambobin jam’iyyar a Jigawa. 

“Muna nan daram cikin goyon bayanmu ga gwamnatin Tinubu, amma mun dagewa kan muhimmancin tabbatar da samun shugabanci mai ƙarfi don inganta haɗin kai da cigaba a cikin APC.”

Jihar Jigawa
Comments (0)
Add Comment