Daga: Ahmed Ilallah
Kusan za a iya cewa an kafa tarihi a game da matsalar wutar lantarkin Nigeria.
A cikin mako guda an samu katsewar wuta a Nigeria kusan sau hudu, kai harma zuwa ga wannan lokaci, wutar lantarkin Nijeriya a cikin kwamacala ta ke.
Shugaba Tinubu, bayan karbar mulki, ya sha alwashin kawo karshen matsalar lantarki a Nijeriya.
Gwamnatin ta Tinubu ta fito da tsare tsare don kawo karshen matsalar data ki ci, taki cinyewa.
Gwamnatin ta cire tallafin wutar lantarki da kadan-kadan, duk ana cewa anyi hakan ne, don ita ce mafitar da zata kara inganta wutar lantarkin.
Babbar damuwar ma, shine na chire tallafi rankatakaf ga kwastomomin da suke kan Rukunin A (Band A), ta yanda kudin ya ninka sama da kashi 200.
Wannan kari ba kawai a kan lantarkin ya tsaya ba, ya taimaka wajen hauhawar firashin kaya, da sake sanya yan Nijeriya cikin ukuba.
Shin lokaci bai yi ba, na wannan gwamnati na sake tunani a kan manufofinta?
Shin dabarun wannan gwamnati zai kai ta ga gaci kuwa?
Duk wannan tsare tsare na gwamnatin Tinubu, sun zamanto ana maganin kabane, kayi na kumbura.
Wannan manufofi, wanda ana yine domin gina tattalin arziki, basa amfani, sai de ma cusa mutane suke cikin azaba.
Domin a game da wutar lantarki, kullum dai baya ake ci.
Duk da cewa, Shugaba Tinubu yace, ya yarda da mashawartansa a harkar tattalin arziki, to dai a kwai matsala.
Don gudun gazawa, da gwamnatin baya tayi, a ka fadi babu nauyi, ya kamata wannan gwamnatin ta hankalta.
In har ana son gyara, ya kamata wannan gwamanati ta sake duban manufofinta, a zahiri dai, basa aiki.
alhajilallah@gmail.com