Ministan Wutar Lantarki na Najeriya, Adebayo Adelabu, ya shawarci Hukumar Makamashin Nukiliya ta ƙasa da kada ta ci gaba da shirin gina sabbin tashoshin nukiliya huɗu da za su samar da megawatt 1,200 kowanne, yana mai cewa akwai buƙatar duba yadda za a fi amfani da makamashin da ake da shi yanzu.
A wata ziyara da muƙaddashin shugaban hukumar, Anthony Ekedewa, ya kai ofishin ministan a Abuja, ya bayyana cewa tun da aka kafa hukumar a 1976, an cimma manyan shawarwari da suka haɗa da tsara amfani da nukiliya wajen samar da wuta, tare da cewa sun kammala nazari a wuraren Geregu a Jihar Kogi da Idu a Akwa Ibom.
Ekedewa ya ce, “Nukiliya na da ƙarfin samar da wutar da za ta wadatar da ƙasa gaba ɗaya,” yana mai ƙari da cewa suna buƙatar haɗin gwiwa da ma’aikatar domin cika wannan buri.
WANI LABARIN: Sanatoci Sun Amince Da Wasu Daga Dokokin Gyaran Harajin Da Tinubu Ya Gabatar
Amma a cewar Adelabu, “Ya kamata mu fara tambayar kanmu yadda muka yi amfani da makamashin da muke da shi na al’ada kafin tsunduma cikin gina manyan tashoshin nukiliya huɗu.”
Ministan ya bayyana cewa, kodayake shirin gina ƙananan tashoshi na nukiliya abin a yaba ne, amma har yanzu Najeriya ba ta kai matakin da za a fara amfani da manyan tashoshi ba.
“Nukiliya ita ce makomar samar da wutar lantarki, amma mu a Najeriya har yanzu ba mu kai ga hakan ba. Muna da buƙatar tsari da haɗin kai tsakanin ɓangarori don amfani da damar da hukumar ke da ita,” in ji shi.
Adelabu ya bayyana buƙatar shirya taron bitar haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatar da hukumar don tsara hanyoyin haɗin gwiwa yadda ya kamata, kamar yadda PUNCH ta ruwaito.