Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce za a samu mummunan farmaki kan Birnin Gaza idan Hamas ta ƙi miƙa makamai da sakin duk fursunonin da suka rage, yana barazanar mayar da birnin tamkar garuruwan da aka ragargaza a baya.
Ya rubuta a shafinsa na sa da zumunta cewa, “Nan kusa, za a buɗe ƙofofin jahannama a kan masu kisan gilla ƴan Hamas,” yana kira ga Hamas ta amince da sharuɗɗan Isra’ila.
Firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa ya umurci fara tattaunawa kai tsaye don sakin fursunoni a lokaci guda tare da shirin ƙwato Birnin Gaza daga hannun Hamas, matakan da ya ce suna tafiya hannu da hannu.
Rahotanni sun nuna cewa an ƙirƙiri wajen ajiyar sojoji na kusan dakaru 60,000 don taimaka wa wannan yunƙuri, lamarin da ya jawo suka daga ƙasashen duniya da kuma damuwa daga cikin gida.
Masu shiga tsakani sun ce Hamas ta amince da wata shawarar sakin fursunoni a tsarin bin matakai, amma Isra’ila na matsa lamba don ganin an saki kowa a lokaci guda, abin da ke kawo cikas ga yarjejeniyar.
Lamarin ya haifar da asarar rayuka masu yawa: harin Hamas na Oktoba 2023 ya kashe Isra’ilawa 1,219, yayin da hukumar lafiya a Gaza mai alaƙa da Hamas ta rawaito cewa, sama da Faldinawa 62,000 aka kashe a hare-haren Isra’ila, yawancin su fararen hula.
Barazanar Katz ta ƙara dagula yanayin tattaunawa kan zaman lafiya yayin da duniya ke neman hanyar kawo ƙarshen kisan ƙare dangin da mayar da fursunoni.