Muhimman Abubuwa 10 Game Da Mummunan Hatsarin Da Ya Faru A Jigawa

  1. Wata tankar man fetur ta yi hatsari a garin Majia, Jihar Jigawa, inda ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 153, inda aka tabbatar da mutuwar 94 nan take a wajen da abin ya faru.
  2. An garzaya da yawancin waɗanda suka jikkata zuwa Babban Asibitin Ringim da Asibitin Gwamnatin Tarayya na Birnin Kudu, yayin da cibiyoyin lafiya ke aiki tukuru wajen kula da dinbin mutanen da suka samu rauni.
  3. Bayan faruwar wannan mummunan lamari, an yi jana’izar mutane 147 a garin Majia, yayin da fiye da mutane 55 suke samun kulawa a asibitoci daban-daban.
  4. Hatsarin ya faru ne lokacin da wata tanka dauke da fetur ta kwace a kusa da Jami’ar Khadija, inda ta yi sanadin tashin gobara lokacin da mutane suka fara kwasar fetur din da ya zube a wurin.
  5. Rahoton Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 147, yayin da ƴansanda suka ce mutane 153 sun mutu, sannan fiye da 100 kuma sun jikkata.
  6. Shugaba Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da sauran manya da dama a ƙasa sun bayyana ta’aziyyarsu, inda Tinubu ya tura tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa yankin da abin ya faru.
  7. Gwamna Umar Namadi ya bayyana wannan lamari a matsayin babban tashin hankali a tarihin Jigawa, kuma ya halarci jana’izar waɗanda suka mutu.
  8. A martani ga hatsarin, Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin sake duba dokokin kula da safarar mai don hana faruwar irin wannan abu a nan gaba.
  9. Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya ta nuna alhini game da wannan masifar, tare da yin kira ga jama’a da su guji ɗaukar matakai masu haɗari kamar kwasar fetur a irin waɗannan wurare.
  10. Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur ta Tarayya ta fara bincike kan lamarin, tana mai bayyana nadamarta kan wannan babbar asarar rayuka.
Jihar Jigawa
Comments (0)
Add Comment