Muhimman Abubuwa Da Ya Kamata A Sani Game Da Ganduje

An haifi Abdullahi Umar a ƙauyen Ganduje da ke cikin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano a 1949.

Ya fara karatun Ƙur’ani da Islamiyya a ƙauyensu, inda ya samu ilimin addini. Ya shiga firamare ta Dawakin Tofa daga 1956 zuwa 1963.

Ganduje ya fara makarantar sakandiren Birnin Kudu a 1964 inda ya kammala a 1968.

Ya shiga makarantar horar da malamai da ke Kano tsakanin 1969 zuwa 1972.

Tsohon gwamnan jihar Kanon ya samu digirinsa na farko a fannin ilmin malanta a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria cikin jihar Kaduna a 1975.

A 1979 ne kuma ya kammala digirinsa na biyu a Jami’ar Bayero ta Kano, sannan ya sake komawa Jami’ar Ahmadu Bello daga 1984 zuwa 1985 don karanta fannin gudanar da harkokin gwamnati.

A 1993 ne ya samu digirin-digirgir daga Jami’ar Ibadan.

Siyasarsa

Ganduje ya shiga jam’iyyar NPN a jamhuriyya ta biyu sannan ya zama mataimakin sakatare na jihar Kano daga 1979 zuwa 1980.

Ya tsaya takarar ɗan majalisar wakilai a 1979 ƙarƙashin jam’iyyar NPN, amma bai yi nasara ba.

A 1998, ya shiga PDP inda ya nemi jam’iyyar ta tsayar da shi takarar gwamna, amma bai yi nasara ba, maimakon haka sai ta tsayar da Rabi’u Musa Kwankwaso.

Amma aka zaɓi Ganduje a matsayin mataimakin Kwankwaso tsakanin 1999 da 2003, sun sake cin zaɓen gwamna da mataimakin gwamna a Kano a shekara ta 2011 zuwa 2015.

A 2015 ne kuma, aka zaɓi Dakta Abdullahi Umar Ganduje matsayin gwamnan Kano, inda ya yi wa’adin mulki biyu daga 2015 zuwa 2023.

BBC HAUSA

Abdullahi Umar GandujeAPC
Comments (0)
Add Comment