Mummunar Ambaliya Da Guguwar Wipha Sun Hallaka Mutane A Philippines, Yayin Da Vietnam Ke Cikin Barazana

Guguwar Wipha da ambaliya sun jefa ɗaruruwan mutane cikin halin rashin matsuguni a Philippines, inda hukumomi suka tabbatar da mutuwar mutane biyar da kuma ɓacewar wasu bakwai, yayin da guguwa ke ƙara matsowa yankin arewacin Vietnam a matsayin guguwa mai tsananin ƙarfi.

Hukumar kula da yanayi ta Vietnam ta bayyana cewa guguwar na tafiya da saurin kilomita 15 a cikin sa’a ɗaya, kuma tana dab da Birnin Haiphong, inda ake hasashen za ta sauka a yankunan Hung Yen da Ninh Binh.

“Mun tanadi sojoji kusan 350,000 domin gudanar da aikin ceto da ba da agaji yayin da ake sa ran ruwan sama na iya kai yawan milimita 500 wanda ka iya haddasa ambaliya da fashewar ƙasa,” in ji hukumar kula da yanayi a ƙasar.

WANI LABARIN: Jihohi 16 Da Suka Ƙi Aiwatar Da Dokar Ƙarin Shekarun Ritaya Ga Malaman Makaranta

A birnin Manila na Philippines, rafin Marikina ya cika ya maƙil har ya fashe tare da tilasta mutane fiye da 48,000 barin gidajensu domin guje wa hatsarin ambaliya, ciki har da wata tsohuwa da direbanta da aka ce ruwa ya cinye su yayin da suke ƙoƙarin tsallaka wata gada.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar ta ce: “An samu motarsu, amma har yanzu ba a gano su ba,” yayin da rahotanni suka bayyana cewa guguwar Wipha na daga cikin guguwowin da suka fi shafar yankuna masu rauni sakamakon sauyin yanayi.

Comments (0)
Add Comment