Muna Nan Kan Bakanmu, Babu Wani Umarnin Kotu Da Ya Hana Mu Yin Zanga-Zanga – NLC

Ƙungiyar Ƙwadago, NLC, ta faɗawa Mai Shigar da Ƙara na Gwamnatin Tarayya kuma Babban Sakataren Ma’aikatar Shari’a cewa, babu wani umarnin kotu daga Kotun Ma’aikata ta Ƙasa ko wata kotu da ya hana ma’aikata ƴan Najeriya shiga cikin zanga-zangar lumanar da ta shirya.

Ƙungiyar Ƙwadagon ta bayyana hakan ne a wasiƙar da ta aikewa Mai Shigar da Ƙara na Ƙasa ta hannun kamfanin lauyoyi na Falana Chambers.

Wannan wasiƙa dai na zuwa ne a dab da lokacin da NLC ta shirya fita zanga-zangar gamagari a duk faɗin ƙasa a ranar Laraba, 2 ga watan Agusta kan cire tallafin man fetur da matsin rayuwar da ya janyo wa ƴan Najeriya, da kuma gazawar gwamnati na fito da hanyoyin magance raɗaɗin da ƴan ƙasa ke sha.

A wasiƙar, NLC ta ce, saɓanin yanda yai zargi kan cewa NLC na ƙoƙarin saɓa dokar kotu ta hana shiga yajin aiki, ƙungiyar ba ta nufin yin hakan, sai dai kuma ta jaddawa Mai Shigar da Ƙara na Ƙasa cewar babu wata dokar kotu da ta hana ma’aikatan Najeriya shiga zanga-zangar lumana a duk faɗin ƙasa.

NLC ta kuma gargaɗi Mai Shigar da Ƙarar da cewar, tun da babu mai iya hana ma’aikata damar da kundin tsarin mulki ya basu na yin zanga-zangar lumana, to ya kamata ya guji yi wa ma’aikatan barazana, da zarginsu da saɓa umarnin kotu.

Gwamnatin TarayyaNLCYajin AikiZanga-Zanga
Comments (0)
Add Comment