Musabaƙar Al-Ƙur’ani ta Duniya ta Saudiyya karo na 45, wadda aka fara a ranar 8 Agusta 2025 kuma aka kammala karatu a 15 Agusta, za a rufe ta a yau Laraba 20 Agusta 2025 “bayan sallar Isha’i a Masallacin Harami da misalin ƙarfe 6:00 na yamma agogon Najeriya.”
Bana ta zo da sabon tarihi inda aka samu halartar ƙasashe 128 da ɗalibai 179, inda masu shiryawa suka jaddada cewa “wannan karo ya kafa sabon tarihi” idan aka kwatanta da shekarun baya.
Ƙididdiga ta baya ta nuna cewa: “a 2020 ƙasashe 73 da ɗalibai 109, a 2021 ƙasashe 103 da 147, a 2022 ƙasashe 111 da 153, a 2024 ƙasashe 123 da 174,” alamar yunƙurin faɗaɗa gasar a ko’ina a duniya.
Sabbin tsare-tsare sun haɗa da “na’urorin mutumtumin robots masu ilimi” don jagoranci da bayar da bayanai ga mahalarta da baƙi a Harami, abin da ya ƙara fasaha da tsari.
An inganta tarbar baƙi da yi musu fassara, sufuri da tanadar cibiyoyin lafiya, tare da haskawa kai tsaye “livestreaming” ta shafukan sa da zumunta da suka bai wa musulmi a duniya damar kallo kai tsaye.
Har ila yau, “an ƙara tsari kan kyaututtuka da rukunan gasar” don ƙarfafa gwiwa, lamarin da ɗalibai suka yaba da shi, suna masu cewa ya “ƙara haskaka musabaƙar da ba da armashi.”
Idanu na kan wakilan Najeriya da ake sa ran za su haskaka a sahun gwaraza, kamar dai yanda aka saba a shekarun da suka gabata.
A bara dai, wani ɗan asalin ƙasar Saudiyya mai suna Saad bin Ibrahim bin Hamd ne ya samu babbar kyautar zama gwarzon duniya a fannin iya karatu, hadda da kuma fassara.
A bana dai, an tanadi kyaututtuka daban-daban da darajarsu ta kai kusan riyal miliyan biyar na Saudiyya kwatankwacin sama kaɗan da naira biliyan biyu domin bayarwa ga mahalarta musabaƙar.