Tun bayan rantsar da Shugaba Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, Najeriya ta fuskanci ƙaruwar tashin hankali, inda aka kashe mutane 13,346 aka kuma yi garkuwa da 9,207 a fadin kasar.
Wannan ƙaruwar tashin hankalin da ta shafi ƙananan hukumomi 667 tana da nasaba da ta’addanci, ƴan fashi, rikicin manoma da makiyaya, da sauran rikice-rikicen zamantakewa.
Rahoton Tsaro na Najeriya daga kamfanin Beacon Consulting, wanda ya ƙware a fannin kula da matsalolin tsaro, ya bayar da cikakken bayani game da wannan lamari.
Rahoton ya ce, daga watan Mayu zuwa watan Disamba 2023, an samu mace-mace 5,802 da sace-sacen mutane 2,754.
A shekarar 2024, lamarin ya ƙara tsananta, inda aka kashe mutane 7,544 aka kuma yi garkuwa da 6,453 daga watan Janairu zuwa Satumban nan.
Masana tsaro suna bayyana damuwa kan ƙalubalen tsaro da ke ci gaba da tsananta, suna kuma kira ga Shugaba Tinubu da ya ɗauki matakai masu ƙarfi don magance matsalar.
Masanan sun jaddada cewa akwai buƙatar inganta tsaron iyakokin Najeriya, musamman na Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, domin hana shigowar ƴan ta’adda daga ƙasashen waje.