Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa, NPHCDA, ta ce, an samu mutuwar mutane 83 a Najeriya yayinda mutane 836 suka kamu da cutar diphtheria daga farkon wannan shekarar kawo yanzu.
Babban Daraktan Hukumar, Faisal Shuaib ne ya bayyana hakan a jiya Litinin a Abuja lokacin da yake ganawa da ƴan jaridu kan matakan kare yaɗuwar diphtheria a Najeriya.
Ya ce, daga watan Mayu na shekarar 2022 zuwa watan Yuli na bana, an samu bayanan zargin kamuwa da cutar har guda 2,455 a jihohi 26, yayinda aka tabbatar da samun cutar a jikin mutane 836 daga ƙananan hukumomi 33 na jihohi takwas da suka haɗa da Cross River, Kano, Katsina, Kaduna, Lagos, Osun, Yobe, da kuma Abuja.
Faisal ya ƙara da cewa, duk da ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na samar da rigakafin diphtheria a ƙasa, har yanzu akwai yara da dama da ba a yi musu ba kwata-kwata ko ba a kammala yi musu rigakafin ba.
Ya ce za a ci gaba da gudanar da rigakafin diphtheria a rukunai guda biyu, inda a rukunin farko da zai fara a ranar 7 ga watan Agusta, za a fara da ƙananan hukumomi 25 daga jihohin Bauchi, Katsina, Yobe da Kaduna.
Ya ƙara da cewa, a rukuni na biyu za yiwa ƙananan hukumomi 171, inda a jihohin Kano, Katsina, Abuja, Yobe, Kaduna da Bauchi za a yi a kowacce ƙaramar hukuma, yayinda za a yi a ƙananan hukumomi 8 na Jigawa, ƙananan hukumomi hurhuɗu a Borno da Osun, sai ƙananan hukumomi uku-uku Lagos, Zamfara da Gombe, da kuma ƙananan hukumomi ɗai-ɗai a jihohin Plateau da Nasarawa.
Cutar Diphtheria dai wata cuta ce da ƙwayoyin cutar bacteria mai suna ‘Corynebacterium’ ke haifarwa, sai dai cutar ta fi kama ƙananan yara musamman na ƙasashe masu fama da talauci.