Na Ceto Tsarin Fanshon Jigawa Daga Rugujewa – Gwamna Namadi

Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fitar da sama da naira biliyan bakwai domin ceton tsarin fansho na hadin gwiwa tsakanin jihar da ƙananan hukumomi daga rushewa, yana mai cewa “ya kamata a fahimta cewa tsarin fansho a jihar Jigawa ya kusa rushewa lokacin da muka hau mulki, mun zuba fiye da naira biliyan bakwai don ceto tsarin.”

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin bikin ranar Ma’aikata ta bana da aka gudanar a Mallam Aminu Kano Triangle dake Dutse, inda ya ce sun fara gyaran dokar tsarin domin magance matsalolin da ke cikinta tare da tabbatar da ɗorewar tsarin.

A cewar Namadi, wannan ne karo na farko da ya yi jawabi kan batun fansho tun bayan ɗarewarsa kan mulki, yana mai amincewa da rahotannin PREMIUM TIMES da suka bayyana giɓin gudanar da tsarin.

A watan Janairun 2024, gwamnatin ta zuba Naira biliyan 2, sai biliyan 3.4 a watan Agusta, sannan ta ƙara da biliyan 1.5 a watan Janairu domin biyan fansho da kuɗin ritaya.

A wata sanarwa daga shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Muhammad Dagaceri, an kori kamfanonin kula da asusun fansho guda biyar saboda rashin ingantaccen tsarin gudanarwa, inda aka naɗa sabbi guda shida ciki har da Premium Pension Fund a matsayin jagora.

A cewar Dagaceri, gwamnatin ta ci gaba da aiki da Norrenberger Pension saboda yadda ya nuna ƙwarewa a baya.

Binciken PREMIUM TIMES ya nuna cewa ƙananan hukumomi 27 ba su biya harajin fansho ba tun daga shekarar 2014 zuwa 2021, inda kuɗin da aka ƙi biya ya kai sama da Naira biliyan 3.2, abin da ya ƙara tabarbarewar tsarin da kuma janyo matsin lamba ga gwamnati.

Comments (0)
Add Comment