Najeriya Ce Kasa Ta Biyu A Duniya Mai Yawan Yara Masu Fama Da Matsalar Karancin Abinci

Yayin wani taron hadin gwiwa, gwamnatin tarayyar Najeriya da kungiyar abinci mai gina jiki ta duniya sun tabbatar cewa yanzu haka akwai a kalla yara miliyan 17 da suke fama da tamowa a Najeriya, lamarin da ya sa Najeriya ta kasance kasa mafi girman matsalar karancin abinci mai gina jiki a nahiyar Afrika ta biyu kuma a duniya baki daya.

An fitar da wadannan alkaluma ne jiya Alhamis 30 ga wata a birnin Abuja yayin taron bayyana sakamakon binciken da aka gudanar na gidaje da iyalai da suke fama da karancin abinci mai gina jiki a kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

A lokacin da take jawabi, daraktar lura da harkokin kiwon lafiya da abinci ta ma`aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya Dokta Bin-Yerem Ukaire ta ce karancin abinci mai gina jiki ya kasance babbar matsalar kiwon lafiyar jama’a a Najeriya duk kuwa da dimbin kudaden da gwamnati ke narkarwa wajen yakar al`amarin.

Ta ce daga cikin manyan abubuwa da ke haifar da rashin abinci mai gina jiki a Najeriya sun hada da rashin ingantaccen  tsarin ciyar da jarirai da kananan yara da rashin karfin ikon samun nau`ikan abinci masu dauke da sinadaran gina jiki da rashin ruwa mai tsafta da kuma ingancin muhalli wanda duka suke da nasaba da talauci.

Dr. Bin-Yerem ta ci gaba da cewa duk da wannan, gwamnati tare da hadin gwiwar abokanan huldar cigaba na kasa da kasa na kokari wajen rage radadin karancin abinci mai gina jiki a kasar baki daya.

A lokacin da yake nasa jawabin yayin taron, daraktan kungiyar abinci mai gina jiki ta duniya a Najeriya Dr. Osita Okonkwo ya ce rashin abinci mai gina jiki matsala ce babba da ya kamata gwamnati ta yi gaggawa wajen samar da mafita.

Dr. Osita Okonkwo ya ce an gudanar da aikin kididdigar gano mizanin wannan matsala ta karancin abinci mai gina jiki a Najeriya ne ta hanyar gwaji kan kananan yara `yan kasa da shekaru biyar dake gidajen talakawa marasa karfin arziki.

Ya ce sakamakon nazarin ya nuna cewa dole ne a kara ingantawa tare da kara tsawon lokacin da za a rinka dauka wajen bayar da kulawa ta musamman ga irin wadannan yara da suke fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki.

Ya bayyana gamsuwa da irin kokarin cibiyoyin kula da lafiyar jama’a, wajen rarraba kayayyakin abinci masu gina jiki ga yaran, amma dai duk da haka kamar yadda ya fada dole ne a kara matsa kaimi wajen sanya ido sosai don tabbatar da ganin kayan suna isa ga ainihin yaran da aka tanada domin su.

Haka zalika ya bada shawarar a kara kulla mu’amalla ta hakika da shugabannin al`umma wajen wayar da kan magidanta mahimmacin amfani da nau’ikan abinci na musamman da aka tanada ga yaran da suke fuskantar matsalar Tamowa a Najeriya.

CRI HAUSA

Karancin AbinciNajeriyaYara
Comments (0)
Add Comment