Najeriya Da Brazil Sun Ƙulla Yarjejeniya Don Inganta Noma A Ƙananan Hukumomi 774

A cikin wani babban mataki na sauya fannin aikin gona a Najeriya, Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannu kan yarjejeniya da Fundação Getulio Vargas (FGV) na Brazil don bunƙasa aikin gona ta hanyar haɗin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu. 

Yarjejeniyar ta mayar da hankali kan samar da takin zamani, fasahar samar da iri mai inganci, da bayar da tallafin kuɗi ga manoma. 

An sanya hannu kan wannan yarjejeniya ne a birnin Rio de Janeiro, Brazil, yayin taron koli na G20, inda Sakataren Dindindin na Ma’aikatar Aikin Gona da Tsaron Abinci (FMAFS), Mista Temitope Fashedemi, ya wakilci Najeriya, yayin da Shugaban FGV, Farfesa Carlos Ivan Simonsen Leal, ya wakilci Brazil. 

Sanarwar da Daraktan Hulɗa da Jama’a, Abiodun Oladunjoye, ya fitar daga Ofishin Shugaban Ƙasa, ta bayyana wannan yarjejeniya a matsayin “sabon matakin haɗin gwiwa na dabaru.” 

Wannan shirin yana cikin aikin Green Imperative Project (GIP), wani shiri mai darajar dala biliyan 1.2 da aka ƙaddamar a shekarar 2018 don zamanantar da aikin gona a Najeriya ta hanyar amfani da ƙwarewar Brazil kan aikin gona a yankunan irin na Najeriya. 

Shirin GIP, wanda Deutsche Bank ke tallafawa, zai ɗauki tsawon shekaru goma, yana mai da hankali kan ƙaddamar da sabbin fasahohin aikin gona da kuma ba da horo ga manoma. 

A cikin shekaru biyar masu zuwa, za a gano kuma a tallafa wa ƙananan hukumomi 774 na Najeriya ta hanyar ba su kayan aiki da kuɗi don samun ci gaba mai ɗorewa. 

“Wannan haɗin gwiwa zai buɗe hanyar da za ta bai wa Brazil damar shiga cikin aikin gona mai cike da kuzari a Najeriya. Tare da FGV, muna shirye don amfani da damar saka hannun jari daga kamfanoni masu zaman kansu don tabbatar da tsaron abinci,” in ji Fashedemi yayin bikin sanya hannu. 

Yarjejeniyar ta tanadi cewa za a samu kimanin dala biliyan 4.3 daga saka hannun jarin kamfanoni masu zaman kansu don cika burin Najeriya na zama mai dogaro da kanta wajen noma. 

Manyan jami’an Najeriya da shugabannin FGV sun halarci wannan muhimmin bikin sanya hannun.

Comments (0)
Add Comment