Najeriya Na Neman Sabon Bashin Naira Tiriliyan 1.2 Da Wasu Basussukan Daga Bankin Duniya

A yanzu haka Gwamnatin Tarayya na tattaunawa da Bankin Duniya kan sabon bashin da ya kai dalar Amurka biliyan 1.5 daidai da naira Tiriliyan 1.2, kamar yanda jaridar PUNCH ta gano.

Gwamnatin na neman bashin ne da a kai wa take da HOPE domin ‘Shirin Bunƙasa Cigaban Ɗan’adam Wajen Samun Damarmaki da Aiyukan Yi’ kamar yanda shafin yanar gizo na Bankin Duniya ya nuna.

Manufar bashin da ake sa ran zai fara aiki a shekarar 2024 bayan samun amincewar bankin ita ce, a bunƙasa harkar samar da ilimi a matakin farko da kuma lafiya a matakin farko ga jihohin da zasu shiga tsarin.

Jaridar ta kuma gano cewar akwai wani sabon bashin da Najeriya ke shirin ciyowa wanda ba a bayyana yawansa ba domin sake fasalin harkokin manyan kuɗaɗe don bunƙasa tattalin arziƙi.

Haka kuma akwai sabbin basussukan guda biyar da Najeriya ke tattaunawa domin samunsu, waɗanda suka haɗa da naira biliyan 231.1 domin shirin samar da mafita ga ƴan gudun hijira da masu masauƙansu.

Sauran sun haɗa da naira biliyan 285.2 domin shirin bunƙasa harkar hada-hadar kasuwancin kayan gona ga mutanen karkara, naira biliyan 577.9 domin shirin bunƙasa samar da makamashi ta sabbin hanyoyin zamani, naira biliyan 539.3 domin shirin samar da wutar lantarki da bunƙasa harkokin noman rani da kuma naira biliyan 285.2 domin shirin bunƙasa samar da abubuwan da ake buƙata don samun ci gaba.

Tun a farko dai, cikin watanni huɗun farko na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Najeriya ta ciyo bashin da yawansa ya kai naira tiriliyan 1.5 daga Bankin Duniya.

Bankin Duniya dai shine kan gaba wajen bai wa Najeriya bashi, inda yake bin Najeriya kusan naira tiriliyan 12 kamar yanda alƙaluma suka nuna a ranar 30 ga watan Yuni, 2023.

A ƴan kwanakin baya kaɗan dai, Ofishin Kula da Bashi, DMO, ya ce bashin da ake bin Najeriya yanzu haka ya kai naira tiriliyan 87.38 a ƙarshen watan Yunin, 2023.

Bashin ya haɗa da wanda Najeriya ta ci daga cikin gida da yawansa ya kai naira tiriliyan 54.13 da kuma wanda ta ciyo daga wajen da ya kai naira tiriliyan 33.25.

Bankin DuniyaBashi
Comments (0)
Add Comment