Najeriya Ta Fi Lagos Tsauri: Tinubu Ya Zama Dole Ya Fifita Ƴan Ƙasa Fiye da Ƴan Kungiyarsa – Farfesa Fagge

Daga Kabiru Zubairu

A wata zuzzurfar hira da jaridar Daily Trust, Farfesa Kamilu Sani Fagge, masanin kimiyyar siyasa daga Jami’ar Bayero ta Kano, ya bayyana yadda wasu gungun mutane ke da tasiri mai ƙarfi a mulkin shugabannin Najeriya, yana mai nuna yadda suke tsoma baki a harkokin gwamnati idan aka kwatanta da yadda ake yi a wasu ƙasashen. 

Da yake magana kan mutanen da ke kewaye da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Farfesa Fagge ya yi bayani kan ma’anar “kitchen cabinet” da “deep state”, wato ƙungiyoyi na sirri da ke tasiri kan manufofin shugaban ƙasa. 

“A yawancin ƙasashen duniya, akwai wasu ƙungiyoyi na hukuma da na sirri waɗanda ke tasiri ga shugaban ƙasa. A baya, ana kiran su da “inner cabinet” ko “kitchen cabinet”, waɗanda suka ƙunshi amintattun shugaban ƙasa. Su ne masu nuna himma sosai wajen yin tasiri kan manufofin da shugaban ƙasa ke yi,” in ji shi.

Ya kuma nuna bambanci mai girma da yadda ake yi a Najeriya. 

“Yawanci, a wasu ƙasashe, waɗannan mutane suna kan doka kuma ana ganinsu a tsarin mulki. Suna yin tasiri amma ba sa tsoma baki yadda muke gani a ƙasashen da ba su ci gaba sosai ba, musamman a nan Najeriya,” in ji shi. 

Ƙoƙarin Kariya Ga Shugaba

Da yake magana kan yawaitar tasirin waɗannan mutanen a shugabancin Najeriya, Farfesa Fagge ya ce waɗannan mutane suna nisanta shugaban ƙasa da al’umma, suna dagula harkokin mulki. 

“Abin da muke gani yanzu shi ne gungun mutane da ke hana shugaban ƙasa mu’amala da jama’a; kuma suna da tasiri sosai. Yawancinsu na kusa ne da shugaban ƙasa ta fuskar alaƙa ta sirri,” in ji shi. 

Ya bayar da misalai na tarihi da suka haɗa da marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari. 

“A zamanin Yar’Adua, akwai wasu mutane masu ƙarfi sosai har ma lokacin da ya yi rashin lafiya ba su bari ƴan Najeriya su san gaskiyar halin da yake ciki ba. Haka ma a lokacin Buhari, akwai wata ƙungiya da ta kasance tana jan ragamar manufofin gwamnati. Har ta kai ga ma’aikatun gwamnati da ake da su bisa tsarin mulki sai sun bi ta gare su (kafin su sami abin da suke so).” 

Mulkin Najeriya Ba Kamar Na Lagos Ba Ne

Da yake magana kan suka da ake yi wa salon mulkin Tinubu, musamman kan tasirin abokan aikinsa daga lokacin da yake gwamnan Jihar Lagos, Farfesa Fagge ya yi gargaɗi kan amfani da manufofin jiha a matakin ƙasa. 

“Gaskiyar magana ita ce, waɗannan mutanen sune waɗanda ya saba aiki da su a lokacin da yake gwamna. Amma yanzu suna ƙoƙarin sa shi ya ɗauki matakin cewa manufofin da ya yi a Lagos za su yi aiki a Najeriya. Wannan ne yasa mutane ke kuka. Najeriya ta fi Lagos tsauri,” in ji shi.

Ya yi kira ga shugaban ƙasa da ya rungumi tsarin hangen nesa, yana mai cewa, “Shugaban ƙasa na Najeriya ne, ba na ƙungiya ba, domin ƴan Najeriya ne suka zaɓe shi, don haka ya kamata ya duba nesa fiye da irin waɗannan mutane.” 

Hanyar Da Za Ta Fitar Da Mu Daga Matsala

Farfesa Fagge ya ba da shawarar cewa dole ne shugaban ƙasa ya fifita ƙa’idojin dimokuraɗiyya da buɗe hanyoyin mu’amala da ƴan Najeriya don sauraron damuwarsu. 

“Hanyar fita daga wannan matsalar ita ce shugaban ƙasa ya gane cewa shi zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ne na dimokuraɗiyya. Dole ne ya zama mai kula da al’ummar Najeriya ba wai wasu ‘yan tsirarun mutane ba,” in ji shi. 

Ya kuma ƙara da cewa, “Duk abin da mutanen suka yi tunanin shugaban ƙasa na so, shi za su sanar da shi; kuma za su rufe masa gaskiya. Don haka ya kamata ya sami wannan ilimi da gaskiya ta wasu hanyoyin … A hukumance, akwai hukumomin tsaro da aka ɗora wa alhakin sanar da shugaban ƙasa halin da ake ciki. Sai kuma a sirrance, yana da sauran hanyoyi da amintattun da ke wasu wuraren.” 

Farfesa Fagge ya kammala da kira ga shugabanci mai bude ƙofa ga kowa da samar da haɗin kai. 

“Idan shugaban ƙasa ko duk wani jagora ya bude ƙofa ga al’umma, sai ya fi masa amfani da ya fi wa ƙasa amfani.” 

Wannan kira na samun shugabanci mai inganci ya zo ne yayin da ƴan Najeriya ke ci gaba da lura da yadda ake yanke shawara a fadar shugaban ƙasa a cikin ƙalubalen tattalin arziki da siyasa.

Comments (0)
Add Comment