Hukumar Kula da Ci Gaban Ƙasashe ta Amurka, USAID, ta bayyana Najeriya a matsayin ƙasa ta biyu a duniya da take fama ƙarancin abinci mai gina jiki.
Daraktar USAID, Anne Patterson ce ta bayyana hakan a jiya Laraba, lokacin da take jawabi a taron Baje Kolin Amfani da Abinci Mai Gina Jiki da Sauran Abubuwan da Bunƙasa Lafiya a Abuja.
Da take kafa misali da binciken da aka gudanar a shekarar 2021 kan samun cin abinci mai gina jiki ta ce, ƙarancin abinci mai gina jiki a tattare da yara ƴan Najeriya ya ƙaru da kaso 12 cikin 100 a tsawon shekaru biyar da suka gabata.
KARANTA WANNAN: Ƴan Najeriya Miliyan 19 Ne Ke Fama Da Ciwon Hanta
Ta ce, wannan ya nuna cewar, Najeriya ce ƙasa ta biyu a fama da ƙarancin abinci mai gina jiki a duniya, sannan ta ce, a tsawon watanni 12 da suka gabata, kaso 2.8 cikin 100 na yaran da ke fama da matsalar ne suka samu tallafin tamowa.
Ta ƙara da cewar, Ƙasar Amurka ta shirya tsaf domin ƙarfafa alaƙa da kamfanoni masu zaman kansu waɗanda ke aiyukan magance ƙarancin abinci.
Babban Sakataren Ma’aikatar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa, Nebeolisa Anako ya ce, ƙarancin abinci mai gina jiki gagarumar matsala ce da ke buƙatar haɗa kai domin magancewa.